2023: Okowa ya zama abokin takarar Atiku a PDP

Daga BASHIR ISAH

Ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ba da sanarwar ɗaukar Gwamnan Jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa.

Wannan na zuwa ne yayin da ya rage ƙasa da sa’o’i 24 kafin cikar wa’adin hukumar zaɓe INEC, kan kowace jam’iyya ta tabbatar da ta miƙa sunayen ‘yan takararta na zaɓen 2023 kada ya wuce Juma’a, 17 ga Yuni.

Atiku ya ba da sanarwar haka ne ranar Alhamis a babban ofishin PDP da ke Abuja.

Ya jaddada cewa haɗin kan jam’iyya na da matuƙar muhimmanci muddin suna son lashe zaɓen 2023, don haka ya ce bai kamata su ɗauki komai da wasa ba.

Daga nan, ya ce ya zaɓi Okowa a matsayin abokin takara ne don su yi aiki tare wajen haɗe kan ƙasa da kuma sake gina ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *