‘Yan majalisu sun nemi a maida murafun magudanan ruwa na titin birnin Abuja

Daga AMINA YUSUF ALI

Majalisar wakilan Nijeriya ta yi kira ga hukumar gudanarwa ta birnin Tarayyar Abuja (FCTA) da ta gaggauta rufe dukkan ramukan saman magudanan ruwa na titi waɗanda suke a buɗe. Domin a cewar su, barin su haka yana jawo asarar rayuka da dukiyoyin al’umma.

Wannan kiran da ‘yan majalisar suka yi ya biyo bayan amincewa da wani ƙuduri da ɗan majalisa, Musa Pali (APC Bauci) ya gabatar a zauren Majalisar a ranar Asabar ɗin da ta gabata a Abuja.

Shi dai ramin saman magudanan ruwa wani rami ne da ake yinsa a saman magudanan ruwa ta yadda masu gyara ko dubawa za su iya shiga ƙarƙashi su duba idan buƙatar hakan ta taso.

Yawanci waɗannan ramukan sukan kasance an yi su ne dai-dai girman yadda mutum zai iya shiga ciki kuma ya iya fitowa idan buƙatar hakan ta taso. Suna da murfi wanda ake iya rufe shi da kuma buɗe shi.

Pali ya bayyana damuwarsa a kan yadda wasu marasa kishin ƙasa sukan sace murafun ramukan shiga ƙarƙashin ƙasa a garin Abuja. Inda hakan yake zama babban haɗari ga masu yiwu da kuma masu tafiyar ƙasa da ba su ji ba, ba su gani ba.

Sannan ya bayyana damuwarsa a kan yadda mutane da dama suka samu munanan raunuka sakamakon faɗawa buɗaɗɗun ramukan saman magudanan ruwa na titi sannan tayoyin motoci da dama sun lalace sakamakon bi ta kan ramukan.

Pali ya ƙara da cewa, tabbas harkar ‘yan gwan-gwan da kuma aikin waɗansu marasa kishin ƙasa shi ne ya jawo satar murafun ramukan saman magudanan ruwar waɗanda ba a kulle su ba ko sanya musu matakan kariya ba.

A kan haka ne ma, majalisar ta yi kira ga jami’an tsaro da su dinga bin sawun masu sace murafun.

Daga ƙarshe, majalisar ta ɗora wa kwamitinta na al’amuran Birnin Tarayyar (FCT) alhakin tabbatar da an yi biyayya ga kiran nasu, sannan su dawo mata da rahoton yadda abin ya kasance bayan sati shida domin ɗaukar matakin da ya dace.