Takarar Sanatan Yobe ta Arewa: APC ta buƙaci INEC ta maye gurbin Machina da Lawan

Daga BASHIR ISAH

Jam’iyya mai mulki (APC), ta aike wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) wasiƙa tana neman hukumar ta ayyana Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan a matsayin ɗan takarar sanata na mazaɓar Yobe ta Arewa a 2023.

Wannan na na faruwa ne bayan da Lawan ɗin ya kasa kai bantensa a takarar Shugaban Kasa, don haka ya buƙaci ya sake komawa Majalisar Dattawa don ci gaba da wakilcin shiyyar Yobe ta Arewa a matsayin sanata.

Duk da cewa Bashir Machina shi ne wanda ya lashe zaɓen fidda gwanin da APC ta gudanar inda ya samu tikitin takarar sanata a shiyyar Yobe ta Arewar, sai kuma ga shi cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 14 ga Yuni da APC ta aike wa INEC, ta nemi hukumar zaɓen ta shaida Lawan a matsayin ɗan takarar a maimakon Machina.

Wasiƙar ta nuna yadda APC ta buƙaci INEC ta maye gurbin sunan Bashir Machina da ya lashe zaɓen fidda gwani da na Sanata Lawan a kundinta.

Jin raɗe-raɗi game da manufar Lawan ɗin a ‘yan kwanakin da suka gabata, ya sanya Machina ƙeƙashe ƙasa kan cewa shi fa ba zai janye wa kowa ba tun da shi ne aka sani a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani.

Machina ya ce yana da ƙwarin gwiwar shugabannin jam’iyya masu bin doka ne waɗanda ba za su aikata abin da ya saɓa wa Kundin Tsarin Mulki da Dokar Zaɓe ba.

Ya ƙara da cewa, yana da tabbacin Lawan ba zai buƙaci sake komawa Majalisar Dattawa ba bayan kammala wa’adinsa a 2023.