Sanatan Arewacin Yobe: Ana taƙaddama tsakanin Sanata Lawan da Machina

Daga MUHAMMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Zazzafar taƙaddama ta kunno kai tsakanin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Sanata Ahmed Ibrahim Lawan, da ɗan takarar Sanatan Arewacin Yobe, Hon. Bashir Sharif Machina; biyo bayan kayen da Sanata Lawan ya sha a zaven fidda gwani shugaban ƙasa da Jam’iyyar APC ta gudanar a makon da ya gabata da kuma nasarar zaɓen fidda gwani da Machina ya samu a ɗaya ɓaren.

Wasu ajiyoyi sun nuna cewa har yanzu Hon. Lawan ya na hararar kujerar tare da bayyana buƙatar Hon. Bashir Sharif Machina ya janye masa, bayan lashe zaɓen fidda gwanin takarar Sanatan Arewacin Yobe, al’amarin da ke ci gaba da ɗaukar hankulan ‘yan Nijeriya.

A daidai wannan gaɓar, al’ummar ƙananan hukumomin Bade da Jakusko a yankin da ke jihar Yobe sun fito kan tituna domin bayyana goyon bayan su ga takarar Hon. Machina, a tsakiyar wannan mako a garin Gashuwa, shalkwatar ƙaramar hukumar Bade.

Dubban jama’ar sun ziyarci fadar Sarkin Bade; Maimartaba Mai Abubakar Umar Suleiman domin miƙa gaisuwar girma tare da bayyana maƙasudin taron, wanda ya ƙunshi mata, matasa da masu ruwa da tsaki a siyasar yankin.

Da yake bayani ga manema labaru jim kaɗan da kammala taron, Barista Hamza Hashimu Karage, ya bayyana cewa, a matsayinsu na al’ummar masarautar Bade, sun yaba da hidimar da Sanata Ahmed Lawan ya yi wa ƙasa na kimanin shekaru 16 a zauren majalisar dattawan Nijeriya, inda har Allah ya kai shi zuwa shugaban majalisar, wanda hakan ba ƙaramin abin alfahari ba ne ga al’ummar masarautar baki ɗaya.

Bugu da ƙari kuma, ya ce: “Muna alfahari da Sanata Ahmed Lawan bisa bajintar da ya yi na takarar kujerar shugaban ƙasa, a Jam’iyyar APC a zaɓen fidda gwani da ya gabata, tare da bayyana baƙin cikin rashin nasarar da ya yi a zaɓen.”

Ya ce, Hon. Bashir Machina gogaggen ɗan siyasa ne wanda ya samu nasarar zaɓen fidda gwani a kujerar Sanatan shiyya ta C, wanda bisa hakan ne muke bayyana cikakken goyon bayan mu gare shi domin samun nasara a babban zaɓe mai zuwa na 2023.

A nashi ɓangaren, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Jakusko, Hassan Kaku Lawan ya bayyana cewa, “wannan taro ne na nuna goyon bayan al’ummar Bade da Jakusko ga ɗan takarar kujerar Sanatan Arewacin Yobe, Hon. Bashir Machina, wanda ya haɗa kowane vangaren jama’a, a matsayin yadda suma al’ummar Machina da sauran ƙananan hukumomin wannan yankin suka nuna wa namu Sanata a baya; Sanata Ahmed Lawan, a shekarun da suka gabata.

“A hannu guda kuma, al’ummar wannan masarauta ta Bade suna bayyana cikakken goyon bayan su ga takarar Hon. Bashir Machina, bisa makamancin irin wannan goyon baya da suka samu daga masarautar Nguru da Machina a lokutan da Sanata Ahmed Lawan ya ɗauka yana riqe da kujerar majalisar dattawan yankin, saboda haka muna goyon bayan sa ɗari bisa ɗari.”

Shi ma tsohon muqaddashin sakataren tsohuwar jam’iyyar ANPP a jihar Yobe, Mohammed D. Sa’idu (Gaskanta) ya tofa nashi albarkacin baki da cewa, “kamar yadda ka ce cin tuwon kishiya ramako, ko shakka babu haka zancen yake. Saboda kimanin shekaru 16 da suka gabata, ita ma masarautar Nguru ta rike kujerar Sanatan Arewacin Yobe, wanda an shirya wannan taron ne domin bayyana goyon bayan al’ummar Bade da Jakusko ga takarar Hon. Bashir Machina a matsayin rama haɗin kai da goyon bayan da suka nuna mana a wadannan shekaru ga Sanata Ahmed Lawan.”

A nashi bayanin, shugaban taron kuma tsohon kwamishina a ma’aikatar wasanni da matasa ta jihar Yobe, Malam Saleh Kachalla ya bayyana maƙasudin taron da cewa, “a matsayinmu na al’ummar Bade da Jakusko; maƙasudin shirya wannan gangamin shi ne domin bayyana goyon bayan mu ga takarar kujerar Sanatan Arewacin Yobe wadda Hon. Bashir Sharif Machina zai yi, muna yi mishi fatan alheri tare da samun goyon bayan mu a babban zabe mai zuwa a 2023.”