Jama’ar mazaɓar Disina a Jihar Bauchi sun koka kan zaɓen ɗan takarar majalisar dokoki

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Jama’ar mazaɓar Disina wacce ke da kujerar majalisar dokoki ta jiha sun gabatar da koken su wa zaɓaɓɓen ɗan takarar gwamnan na Jam’iyyar APC, Shugaban rundunar mayaƙa sama na askarawar tarayyar Nijeriya mai ritaya Sadique Baba Abubakar da ya yi wa Allah da Annabi ya duba batun zaven fitar da ɗan takara da aka yi a mazaɓar Disina na shiga majalisar dokoki ta jiha, da zummar daidaita lamarin maguɗi da aka tafka a cikin zaɓen.

A wani taron yin jaje da muryar gudanar da gurɓataccen zaɓen da aka yi a kwanakin baya a ranar Lahadi da ta gabata, jama’ar mazaɓar Disina sun nuna matuƙar kaɗuwa da damuwar su dangane da danniya wa maras ƙarfi da aka yi a yayin gudanar da zaɓen na takarar shiga majalisar dokoki ta jiha wa ɗan takarar su, Hon. Yakubu Ali Disina.

Daraktan kamfen na ɗan takarar shiga majalisar, Dokta Armaya’u Alhaji Sani ya nuna matuƙar damuwar sa bisa yadda ranaku uku kafin zaven aka killace masu jefa ƙuri’a har na tsawon kwanaki uku a cikin wani gida dake cikin garin Disina, yadda ko da zuwa masallaci sai tare da yi masu rakiya har zuwa ranar zaɓe da aka yi zaɓen wakaci-ka-tashi na murɗiya, haɗi da bai wa wani abokin adawa nasarar zaɓen bisa son zuciya da rashin sanin ya kamata.

“Zaɓe ne na jeka-na-yi-ka na fitar da ɗan takarar shiga majalisar dokoki a mazaɓar Disina aka gudanar, zaɓe ne na soki-burutsu, na mai ƙarfi shi zai yi kaye, na kange masu jefa ƙuri’a, tsoratarwa da tirsasawa har na tsawon kwanaki uku a cikin wani gida tamkar ‘ya’yan tattabaru harya zuwa ranar zaɓe da aka ayyana wanda ake so ya ci zaɓen,” inji Armaya’u.

Don haka, Armaya’u ya jawo hankalin ɗan takarar gwamna na jihar Bauchi a ƙarƙashin tutar jam’iyyar APC, Ambasada Sadique Baba Abubakar daya shiga cikin wannan lamari da zummar an kawo maslaha a cikinsa, yana mai yin tuni da cewar: “Abinda nake tsoro a cikin wannan lamari shine a tirsasa masu jefa ƙuri’a su jefawa wani ɗan takara daban bana jam’iyyar mu ba a ranar zaɓen gamagari. Domin mu dai, muna nan daram a cikin jam’iyyar APC, babu batun canjin sheƙa.”

Dokta Armaya’u ya yi tuni da cewar: “A ranar zaven fitar da ɗan takara, na buƙaci taimakon jami’an tsaro na SSS da su yi Allah da Annabinsa, su je su fito da daliget domin a yi zaɓe na gaskiya ko da za a kayar da ɗan takarar mu ne, amma yin hakan ya faskara, aka yi abinda aka yi na son zuciya, na qin gaskiya, Allah kabi mana kadi.”

Shi ma da yake yin jawabi, ɗan takar da aka danne, Honarabul Yakubu Ali Disina ya bayyana cewar, ya sayo takardar shiga takara na Jam’iyyar APC na kuɗi Naira miliyan biyu har ma da na ayyana shiga takara na Naira dubu hamsin tare da bin dukkan ƙa’idojin jam’iyyar na shiga takarar zaɓe, amma sai aka yi zaɓen bingi-bingi, aka murɗe masa ‘yancinsa.

Wata mata mai goyon bayan Jam’iyyar APC, Suwaiba Ibrahim da take yin tsokaci bisa lamarin, ta bayyana rashin jin daɗin ta dangane da fin ƙarfi da aka yi wa Yakubu Ali Disina, tana mai tuni da cewar, irin haka ma ta faru ga Yakubu Ali a shekara ta 2019, tare da fatar Allah ya yi masa sakayya. Ta kuma jaddada cewar, suna nan daram a cikin Jam’iyyar APC, babu gudu, babu ja da baya.