Jam’iyyar ADC ce mai manufofin taimakon talakawa – Kwamared Haruna Wakili

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Ɗan takarar Majalisar Tarayya a ƙarƙashin Jam’iyyar ADC a Ƙaramar Hukumar Fagge, Kwamared Haruna Kabiru Wakili ya ce jam’iyyar na da kyakkyawar manufofi na kawo cigaba ga rayuwar talakawa.

Ya ce tun farko su suka jago-jago da jam’iyyar suka raineta wajen wayar dakan jama’a suka ginata, inda ya kuma zama shugabanta na jiha mafi ƙarancin shekaru; shine kuma ya gayyato Sheik Ibrahim Khalil wanda yake mata takarar Gwamna a Jihar Kano.

Ya ce jam’iyyu manya da ake da su sun lura ba sa bai wa matasa dama don kawo sauyi. Don haka suka ɗauki ADC kuma mutane sun biyosu da tunanin cewa za a iya kaiwa gaci na kawo sauyi saboda a da basu wuce su uku ba da suka yarda da ADC, amma yanzu a cewarsa tafiya ta yi nisa, tunda a cewarsa jam’iyyar yanzu haka tana gogayya da saura.

Kwamared Haruna Kabiru Wakili ya ce jam’iyyar tasu ta ADC tana da manufofi na gina matasa da magance shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da ba su aikin yi da inganta ilimi tun daga tushe har zuwa sama.

Haruna Kabiru Wakili ya ƙara da cewa kusan shekaru 20 yana siyasa a cikin shekarunsa 37 a yanzu sun sha tura mutane amma basa cika alƙawari na buƙatun al’umma, sai wasu suka nemi lallai su zo su bada gudunmuwa ta tsayawa takara tunda suna gani zai iya.

Ya ce akwai wata ƙungiya ta matasan ‘yan siyasa a Fagge, da farko da suka same shi akan ya yi takara ya ce ba zai yi ba saboda ganin yanayin siyasar ƙasar ta gurɓace ba za a iya kawo gyara ba, amma bayan da suka matsa da nuna yarda da irin gudunmuwar da yake bayarwa, don haka ya amince ya shiga harkar neman takarar ɗan majalisar tarayya na Fagge kuma kullum tafiyar cigaba take mutane matasa maza da mata suna cigaba da ba shi goyon baya.

Kwamared Haruna Kabiru Wakili ya ce takarar tasa ta ‘yan ƙaramar hukumar su ta Fagge ce ba ta sa ba ce, domin a cewarsa bai taɓa tunanin zai yi takara a 2023 ba.

Kwamared Haruna ya ce a ƙaramar hukumar Fagge za a soma bada misali na cancantar mutum ba jam’iyya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *