Saƙon Xi ya ƙarfafa gwiwar matasan Afrika wajen raya hulɗar Sin da Afrika

Daga CMG HAUSA

Aikewa da sakon da Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar jamiyyar kwaminis ta ƙasar Sin ya yi cikin lokaci, ga wasiƙar da mahalarta taron ƙarawa juna sani na ƙungiyar ‘yantar da kudancin Afrika na shekarar 2022, ya yi matuƙar ƙara ƙaimi ga matasan Afrika.

Nawanda Yahya, jagoran mahalarta taron daga ƙasar Tanzania, ya bayyana cewa, samun sakon amsa daga shugaba Xi cikin ƙasa da mako guda, wani kwarin gwiwa ne ga bangarorin matasan Afrika, da shugabannin da suka halarci taron na makonni biyu, a makarantar nazarin mulki ta Mwalimu Julius Nyerere, dake gundumar Kibaha a gabar tekun ƙasar Tanzania.

Shugabannin makarantar tare da haɗin gwiwar jamiyyu shida na kudancin Afrika da suka haɗa da, jamiyyar CCM ta Tanzania, da jamiyyar ANC ta Afrika ta kudu, da jam’iyyar ‘yantar da Mozambique, da jamiyyar ‘yantar da jama’ar Angola, da jam’iyyar SWAPO ta Namibia, da kuma jam’iyyar ZANU-PF ta Zimbabwe.

Marcelina Chijoriga, shugabar makarantar Mwalimu Julius Nyerere ta yi martani tare da nuna amincewa da samun saƙon wasiƙar daga shugaba Xi, inda ta ce, wannan wani babban alamari ne wanda ke ƙara haifar da kyakkyawan fata ga matasan jamiyyu shida na Afrika, har ma da nahiyar Afrika baki ɗaya.

Mai fassarawa: Ahmad daga CMG Hausa