Sallah: Sarkin Zazzau ya dakatar da hakimai huɗu

Spread the love

Daga SADA LABARAN a Zariya

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya dakatar da wasu hakimai huɗu na Masarautar Zazzau daga muƙamansu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun Fadar Zazzau, Abdullahi Aliyu Ƙwarbai ya fitar jim kaɗan bayan sauka daga hawa ranar sallah, an dakatar da hakiman ne bisa saɓa dokokin da aka gindaya na Hawan Sallah.

Hakiman da aka dakatar sun haɗa da Ubangarin Zazzau Alhaji Bashir Shehu Idris da Wakilin Birnin Zazzau Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo da Sarkin Dajin Zazzau Alhaji Shehu Umar da kuma Garkuwan Kudun Zazzau Alhaji Muhammadu Sani Uwais.

Ana zargin hakiman da saɓa doka ta uku da ke cikin kundin laifukka da hukunce-hukuncen hawa a Masarautar Zazzau wadda ta haramta wa kowane hakimi yin hawa da ‘yan tauri riƙe da makamai.

By Editor