2023: Gwamna Bala ya buƙaci ’yan Nijeriya su wancakalar da APC

Spread the love

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ya bayyana cewar, ba za su naɗe hannayen su, su ƙyale suna kallo ana kisa da satar mutane a kullum a sassan ƙasar nan ba, ba tare da sun ce cas ba.

Don haka, Gwamnan sai yayi kira ga ‘yan Nijeriya su fito ƙwansu da ƙwarƙwatarsu a ranar zaɓen gamagari domin su wancakalar da jam’iyyar APC mai riqe da kambun mulkin tarayyar Nijeriya dake matakin ƙoli ta ƙasa da zummar kawo ƙarshen barazanar rashin tsaro a ɗaukacin faɗin ƙasar nan.

Mohammed, wanda kuma yake neman shiga takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam’iyyar PDP, ya bayar da tabbacin cewar, rashin tsaro da a kullum yake yi wa ɗaukacin jama’ar ƙasar nan barazana zai gushe matuƙar jam’iyyar PDP ta kama ragamar mulkin Nijeriya a shekara ta 2023.

Da yake yi wa manema labarai jawabi yayin da ya kai ziyarar gaisuwar sallah wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Mohammed Maqarfi, Gwamna Bala ya ce hanya mafi sauƙi na kawar ƙalubalolin rashin tsaro a ƙasar nan shi ne a yi waje da gwamnatin da a yanzu take kan karagar mulki.

Ya ce, “kai ka taɓa ganin irin wannan matsancin yanayi da ƙasar nan take ciki a halin yanzu a ƙarƙashin shugabancin jam’iyar PDP? Mun mulki ƙasar nan har na kimanin shekaru 16 ba tare da fuskantar irin wannan yanayi na baya tsiya gaba tsiyaki ba.

“Faufau, ba a mu naɗe hannayen mu muna kallon ana kisan waɗanda ba su ji, ba su gani ba ala-kulli-yaumin, tare da satar mutane kullum, ba tare da mun yi abinda ya kamata ba, a gaskiya fa tura takai bango.

“Mu dukkan mu shaidu kan abubuwan da suke faruwa a ƙasar nan, kuma domin haka ne muke gabatar da kawunan mu, domin tsinkayar nagari daga cikin mu, waɗanda za su fitar da kitse daga wuta, domin mu tsamo ‘yan Nijeriya daga tartatsin waɗancan shugabanni masu alfahari da girman kai, masu tsiwa da ƙasaita na rashin taɓuka komai wa jama’a”.

Sai ya misaltawa manema labarai, “ba ku nanne a Kaduna lokacin da Gwamna Ahmed Maƙarfi yake mulki? Babu tashin-tashinar addini ko ƙalubalen rashin tsaro.

“Ku yi dubi da abubuwa da muke gudanar wa a jihar Bauchi man. Muna guzawa, muna da tsari da kintata lamuran tsaro, domin mu tabbatar da tsaro da rayukan jama’a.

“Mukan gwamutsi al’ummomin mu daban-daban, hakazalika masarautun gargajiyoyin mu, haɗi da masu ruwa da tsaki.

“Dukkan waɗannan batutuwa da muke ambato babu su a tsarin gwamnatin da take kan karagar mulki. Kuma rashin ire-iren waɗannan ma’amaloli suna daga cikin gaggan batutuwa masu wanzar da rashin tsaro, haɗi da tashin tashinoni da iƙirarorin neman ɓallewa a wasu shiyyoyin ƙasar nan.

Da ya karkata zuwa wajen babban taron ƙasa na jam’iyyar su ta PDP kuwa, sai gwamnan na Bauchi ya ce, “ka da fa a mance, mun yi jagoranci wa ƙasar nan na tsawon shekaru 16. Idan aka duba tarurrukan mu na baya kuwa, za a yi la’akari da cewar, an gudanar da komai a bisa tsari, babu kace-nace.

“Hakan ya kasance ne saboda ba batu ne na burace-buracen mutum ɗaya ba, abinda muke buƙatar gani a matsayin masu neman shiga takarar shugancin ƙasar nan, dama waɗanda za su yi zaɓen su, shi ne taron zaɓe mai inganci kuma karɓaɓɓe wa kowa da kowa.

“Kuma muna shirye da mu yi aiki da kowane mahaluƙi da ya yi nasarar samun zaɓen sa, ba tare da son zuciya ba. Shugabancin jam’iyyar dai a halin yanzu ya bai wa kowa damar farauto ƙuri’u daga kowane sashe na ƙasar nan, gabanin babban taro da jam’iyyar za ta gudanar.”

By Editor