Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Tsohon mataimaki na musamman kan yaɗa labarai a kafofin sadarwa na zamani, Salihu Tanko Yakasai, ga Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana aniyarsa ta tsaya wa takarar Gwamnan Jihar Kano a zaɓen 2023 da ke tafe.
Yakasai ya bayyana hakan ne cikin wani saƙo da ya wallafa ranar Talata a shafinsa na Tiwita.
Tsohon hadimin gwamnan wanda aka fi sani da Ɗawisu ya ce zai ayyana takararsa a hukumance a yau Juma’a.
Wannan na zuwa ne makonni bayan ficewarsa daga jam’iyyar APC, inda ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar PRP.
Idan ba a manta ba a watan Fabrairun 2021 ne Gwamna Ganduje ya sauke shi daga muƙaminsa bisa dalilin maganganun da gwamnati ta ce ba su kamata ba da kuma sukar Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.