Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawa ya sayi fom na takarar Gwamnan Kebbi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Ranar Laraba da ta gabata ne tawagar shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi mai wakiltar mazavar Kebbi ta Arewa a qarkashin jagorancin  Alhaji Sani Dododo (Tambarin Gwandu) da Alhaji Bello Bagudu, Alhaji Rabi’u Qaura da kuma babban hadimin sa Alhaji Bilyaminu Bawale  ta buɗe fagen sayen fom na don neman takarar kujerar gwamnan jihar Kebbi a babbar shalkwatar jam’iyyar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Da ya ke zantawa da manema labarai shugaban kwamitin gudanarwa na siyasar Sanatan Alhaji Aliyu Gandu Augie ya bayyana cewa yin hakan ya biyo bayan  karva kiraye-kirayen da  al’ummar gundumar Kebbi ta Arewa da kuma jihar Kebbi bakiɗaya ke yi wa shugaban masu rinjaye Sanata Dokta Yahaya Abubakar Abdullahi da bayan kammala wa’adin sa na biyu a majalisar dattawa ya kamata ya dawo ya jagoranci jihar Kebbi saboda ya fitar da ita daga halin da ta tsinci kanta na ɗaya daga cikin jihohi mafi koma-baya daga cikin jihohin Nijeriya wanda ba shakka bisa ga la’akari da irin gudummawar da ya ke bayarwa a zauren majalisar dattawa ana ganin zai iya ceto jihar ta Kebbi.

Ya ƙara da cewa sanin kowa ne idan dai dattijantaka da cancanta ake nema to shi ne ya fi dacewa, bayan wannan kuma idan za a iya tunawa yana daga cikin limaman siyasar jam’iyyar APC waɗanda suka yi renon ta a jihar Kebbi har ta kawo inda ta ke a yanzu.

Dangane da maganar sauya jam’iyya kuma, Alhaji Aliyu Gandu Augie ya ce ba gudu ba ja da baya yana nan a jam’iyyar APC “saboda ba za mu gina gida ba sannan kuma daga baya mu fice mu barwa waɗanda suka same mu a ciki ba. Saboda haka muna nan jam’iyyar APC kuma mu masu biyayya ne ga shugabanni da dokokin jam’iyya hasali ma saboda soyayyar sa da jam’iyyar APC shi ne mutum na farko da ya soma sayen fom a zahiri wanda idon duniya ya shaida.” 

Alhaji Gandu ya yi kira ga al’ummar jihar Kebbi bakiɗaya musamman ‘ya’yan jam’iyyar APC da ƙasa su ji tsoron duk wata barazana su ƙara ɗamara don bai wa Sanata Dokta Yahaya goyon bayan su tare da addu’o’in samun nasara da kuma zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar nan bakiɗaya kuma su guji duk wani abu da zai kawo tashin hankali. 

By Editor