Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu ‘yan uwa guda biyu a Lahadin da ta gabata sun rasa rayukansu a ƙoƙarin ɗauko wayar salula da ta faɗa cikin masai a Jihar Kano.
Rahotanni sun bayyana cewa mutum na farko, mai suna Haruna Abdullahi mai shekaru 30 da haihuwa, shi ya fara shiga cikin shaddar domin ya ɗauko wayarsa da ta faɗa.
Lamarin dai ya afku ne a ƙauyen Aku da ke Ƙaramar Hukumar Gaya ta jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa yayin da Marigayi Abdullahi ya shiga shaddar domin ɗauko wayar ta sa, sai ya maƙale ya kasa fitowa, lamarin da ya riƙa neman a kawo masa agaji.
Shaidun gani da ido sun ce Abdullahi na cikin wannan halin ne sai yayansa, mai suna Adamu Ɗanjimmai, mai shekaru 45, ya shiga masan domin ceto ƙanin nasa, inda shi ma ya maƙale, sai su ka rasu gaba ɗaya.
A cewar mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi PFSII, ya ce sun sami kiran gaggawa a ofishin su na Gaya da misalin ƙarfe 7:15 na safe daga wani Ali Ahmad wanda ya sa suka garzaya wurin cikin gaggawa.
“Da isa wurin da misalin ƙarfe 7:25 na safe, mutanenmu sun gano wasu mutane biyu da aka ruwaito ‘yan uwan juna sun maƙale a cikin wani rami na shadda.
“Shaidu da suka shaida idanunsu sun tabbatar da cewa wanda ya rasu na farko ya shiga cikin ramin ne don ɗauko wayarsa da ta faɗa, yayin da ɗan uwansa da ya je ceto shi shi ma ya kasa fitowa har ta Allah ga kasance.”
Abdullahi ya tabbatar da cewa an fito da dukkan Waɗanda abin ya rutsa da su a sume kuma daga baya aka tabbatar sun mutu, yayin da tuni aka miƙa gawarwakin ga hakimin ƙauyen Aku Adamu Isyaku domin binne su.
