Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano
Shugaban Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kano, Dakta Kabiru Ahmad Gwarzo, ya bayyana cewa samar da cibiyar yin katin zaɓe a harabar kwalejin ya taimaka matuƙa wajen sauƙaƙa wa ma’aikata, ɗalibai da maƙotan makarantar samun damar mallakar katin zaɓe ko gyara wanda ya lalace.
Dakta Gwarzo ya ce kwalejin ta haɗa kai da Hukumar Zaɓe ta ƙasa mai Zaman Kanta (INEC) domin samar da wannan cibiyar, wadda za ta riƙa yi wa ɗalibai, ma’aikata da al’ummar da ke makwabtaka da kwalejin rajista da gyaran katin zaɓe cikin sauƙi.
Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai, inda ya ce matakin ya biyo bayan kiran da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo da sauran masu ruwa da tsaki suka yi na cewa kowa ya bada gudummawarsa wajen wayar da kan jama’a kan muhimmancin katin zaɓe.
A cewarsa, mahimmancin katin zaɓe ba wai a siyasance kaɗai yake ba, har ma yana da tasiri a fannonin ilimi da ci gaban al’umma baki ɗaya. “Mun yanke shawarar kafa wannan cibiyar ne domin kada ɗalibanmu da ma’aikatanmu su fuskanci wahala ko jinkiri wajen yin rajista. Haka kuma muna son al’ummar da ke makwabtaka da mu su amfana,” in ji shi.
Shugaban kwalejin ya ƙara da cewa katin zaɓe ne ya bai wa al’ummar Kano damar zaɓar shugabanninsu, ciki har da zaɓen Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a lokuta daban-daban. Ya ce tarihin da waɗannan shugabanni suka kafa a fannin ilimi da sauran ci gaba ya isa ya zama darasi ga jama’a kan muhimmancin katin zaɓe.
Dakta Gwarzo ya buƙaci ɗalibai da ma’aikata da su yi amfani da damar da aka samar musu, tare da jaddada cewa mallakar katin zaɓe na daga cikin hakkokin ɗan ƙasa da kuma alhakin da ya rataya a wuyansa.
