Sanata Shekarau ya koka kan mayar da su saniyar ware a harkokin APC ta Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai ci, Sanata Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano), ya ce sun shigar da kukansu ga uwar jam’iyyarsu ta APC kan yadda ya ce ana gudanar da harkokin jam’iyyar tasu ba tare da sako su ciki ba.

Shekarau ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar wadda Manhaja ta samu kwafinta.

Cikin sanarwar, Shekarau ya soma ne da miƙa godiya ga Allah da kuma salati ga Manzon Allah (SAW) albarkacin bikin Maulidi, kana daga bisani ya bayyana halin da ya ce jam’iyyar APC ta Kano ke ciki.

A cewarsa, “Ni Sanata Ibrahim Shekarau, na jagoranci wasu daga cikin waɗanda aka zaɓe mu, daga majalisar ƙasa. Mun shigar da kuka ga uwar jam’iyya a kan rashin gudanar da abubuwan da suka shafi jam’iyya tare da mu. Mu zaɓaɓɓu ne, jama’armu suna da haƙƙi.”

Ya ci gaba da cewa, “An karɓi ƙorafinmu da mutuntawa, kuma mun gode. Muna fatan a warware taƙaddamar cikin lumana.”

Shekarau ya ce yana nan cikin jami’yyar APC daram-daƙam inda za a ci gaba da gwagwarmaya tare da su har illa masha Allahu.

“Ina sanar da duk jama’armu, ina cikin jam’iyyar APC daram-dam, za mu tsaya har illa Masha Allahu. A wannan tafiya tamu babu cin mutunci, babu zagi, ba wulaƙanci.

“Mun yi haƙuri amma ba za mu lamunci sakarci ba. Ƙorafinmu yana gaban mahukunta. Ba za mu saurari kowa ba sai waɗanda muka kai musu kuka”, in ji shi.

Kazalika, ya ce “A jihar Kano Alhaji Ahmadu Haruna Zago shi ne shugaban jam’iyyar APC zaɓaɓɓe a gurinmu. Muna yi masa addu’ar Allah ya ƙarfafi zuciyarsa kuma Allah ya taya shi riƙo. Sauran waɗanda aka zaɓe su tare da shi su 35 muna addu’ar Allah ya yi musu jagora.”

A ƙarshe, Shekarau ya yi fatan Allah Ya taimaki Najeriya da jihar Kano da jam’iyyar APC da ma shugabanni a matakai daban-daban.