Matsalolin da ke tattare da aikin jarida a wannan lokacin – Abdulkarim Mohammed

“Dole ne ɗan jarida ya san mene ne buƙatar ƙasa a aikinsa”

Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano

A wannan lokaci aikin jarida ya shiga wani yanayi da a ke ganin yana cike da ƙalubale ta ɓangarori da dama, ta yadda a ke kasa gane labarin gaskiya da na ƙarya da sauran matsaloli masu tarin yawa. Abdulkareem Mohammed tsohon ma’aikacin jarida ne a fannin rediyo da talbijin, wanda ya shafe sama da shekaru 40 yana gudanar da aikin. A yanzu shi ne shugaban kamfanin ‘Movie Image’ da ya ke gudanar da harkokin yaɗa labarai. Wakilin mu a Kano Mukhtar Yakubu ya tattauna da shi dangane da yadda aikin jarida ya ke a ilmance da kuma yadda a ke gudanar da shi a wannan lokacin, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:

Malam Abdulkareem Muhammad, kana daga cikin mutanen da suka daɗe a fagen aikin jarida a ƙasar nan. Zamu so ka yi wa masu karatun mu bayani a kan aikin jarida a yadda ya ke a ilmance da kuma yadda a ke gudanar da shi a yanzu.
To shi aikin jarida wani vangare ne na musamman da ya ke buƙatar cewa, wajibi ne mutum ya karance ya laƙance shi har ya mayar da shi ya zama sana’a. Kuma ba a mayar da duk wata harkar aiki a matsayin sana’a, sai na farko idan tana da hurumin da za a duba a ga cewar idan mutum yana son ya karance ta a gurbin ina da ina a ke son a yi amfani da ita. Saboda haka aikin jarida ya faɗa a wannan muhallin, saboda za ka iya yin sa a diploma qarama da kuma babba, za ka iya yin sa a digirin farko da na biyu, har zuwa na uku, kai za ma ka iya zama farfesa duk a karatun aikin jarida. Saboda haka ka ga a ilmance aikin jarida ya samu hurumin ilimi.

Sannan a kan mataki kuma mutum zai shiga aikin ne kamar na share fage yadda za ka yi ta girma kuma ka haɓaka har ka kai matsayin da za a ce maka ko Janar Manaja ko Manajan Darakta ko Babban Sakatare, idan ma ka bunƙasa har ma sai ka kai ga Kwamashina, ko ma ka tsallake ka tafi minista. Saboda haka a fannin aiki ka ga yana da wannan hurumin.

Sannan a tsarin mulki na ƙasa, akwai wato turaku guda uku a matakai, akwai Gwamnatin Tarayya da ta jiha, Majalisa sannan akwai ɓangaren Shari’a. sai kuma aka ware wa aikin jarida ɓangare ya zama shi ne na huɗu. Waɗanda za su rinƙa saka ido a kan waɗanan ɓangarori guda uku da a ke da su na tafiyar da aikin mulki, sun zama kamar Alƙalin wasa kenan wanda ya ke da usur a hannun sa, su za su yi magana a dawo kan hanya idan sun ga masu gudanar da mulki sun yi ba dai-dai ba. To ka ga ko ta wannan za a gane aikin jarida wani abu ne da ya ke da muhimanci na daban.

To, a can baya ku da ku ka fara aikin kusan gidajen rediyo, talbijin da kuma jaridu duk mallakar gwamnati ne. Amma a yanzu an samu bunƙasar kafofin yaɗa labarai masu zaman kan su, wanda hakan ya sa aikin ya bunƙasa ya kai wani mataki. Ko ya ka ke kallon yadda bunƙasar kafofin yaɗa labarai su ke a wannan lokacin?
To da farko dai ni na fara aikin jarida a shekara ta 1979 a gidan talbijin da rediyo na Jihar Kano, to a wancan lokacin ina tabbatar maka ba ma za ka kalli talbijin ba, sai lokacin da NTA ta buɗe tasha, kuma a lokacin sai ƙarfe huɗu na yamma a ke buɗe tashar zuwa ƙarfe sha biyu na dare, kuma daga an rufe shikenan sai kuma gobe. To amma a yanzu kamar yadda ka faɗa yanayi ya canza.

Na biyu kuma a wancan lokacin, duk wani shiri da za a yi, na gwamnati ne, da kuɗin gwamnati za a yi, saboda haka a gwamnati ce za ta tsara yadda ɗan kallo zai gani kuma a haka ɗin za a aiwatar da shi ko na rediyo ne ko na talbijin ne ko na jaridar ne. To daga 1982, shi ne aka bada umarni cewa ban da gidajen rediyo da talbijin na gwamnati an ba da ikon cewa duk wani ɗan ƙasa wanda ya bi ƙa’idar da aka shimfiɗa zai iya neman izini a ba shi damar ya kafa na sa na kan sa. Kuma daga wannan lokacin zuwa yanzu an samu hayayyafar kafofin yaɗa labarai ya wuce waɗanda a ke da su a baya fiye da yadda a ke tsammani. To ka ga an samu cigaba ta wannan harkar, wanda ya kasance mutane da yawa sun samu gurbin ayyuka da aka ɗauka aiki a wannan gidajen yaɗa labaran wanda ya ke mallakar ‘yan ƙasa ne.

A yanzu kafafen yaɗa labarai sun yi yawa. Amma kuma yanayin aikin yana da tarin matsaloli ko me ya sa hakan?
Abin da ya sa shi ne, wanda ya ke da gidan rediyo ko talbijin ko jarida kowa yana da irin ta sa manufar don haka ba zai zama ɗan amshin Shata ba ne, in kuma ya zama, to ba zai samu mutane masu bibiyar sa ba. Saboda haka zai duba ya ga mene ne mutane su ke so su ji, yadda zai riqe su a matsayin abokan huɗɗar sa, saboda ita harka ta yaɗa labarai dole idan mutum yana gudanar da shirye-shiryen sa, ya yi la’akari da abin da mutane su ke so. To amma a yin haka ɗin, saboda aikin jarida akwai matakai da a ke ɗauka don haka sai an duba an tantance abubuwan da a ke yaɗawa jama’a a ga bai kassara su ba. To ka ga yawanci za ka ga ta kafofin yaɗa labarai na gwamnati, su sun fi taka tsan-tsan a kan wannan. Su kuma waɗanda na ‘yan kasuwa ne, za ka ga cewa kasuwar su ke bi saboda mutane. To ka ga bambancin kenan.

A ɓangaren kafofin yaɗa labarai masu zaman kan su, kana ganin ƙoƙarin samar da kuɗaɗen gudanar da aikin shi ne ya haifar da rashin tsari a cikin aikin jarida, ko ya ka ke kallon wannan maganar?
To na farko dai ita hukumar da ta ke kula da kafafen yaɗa labarai wato NBC ita ce hukumar da ke da alhakin ta duba ta ga mene ne sha’awar gwamnati a kan harkar yaɗa labarai? Waɗanne ƙa’idoji ne za su gindaya masu gudanar da wannan aikin su bi shi domin ƙasa ta zauna lafiya. To akwai su, kuma na san cewa da yawa za ka ji cewa gidan rediyo kaza ko gidan talbijin kaza an ci su tara, saboda ba su bi wannan ƙa’idar ba. To amma duk da haka saboda yunƙuri da su wannan gidajen jaridu masu cin gashin kan su, suna ganin cewar tun da ba gwamnati ba ce ta ke ba su kuɗaɗen tafiyar da aikin su dole sai sun bi abin da masu kallo su ke so saboda su jawo hankalin su, su samo kuɗin talla da za a samu a gudanar da aikin yadda zai tafiyar da kamfanin, to wannan ya sa su kan ɗan shagala, amma dai duk da haka ana saka musu ido idan aka ga wani ya tsallake iyaka sai a jawo masa linzami a ci shi tara, kuma tana ma da hurumin ta ce ta rufe wajen. Ko kuma idan ka zo za ka sabunta lasisi a ce an hana ka. Saboda haka dole mutane suna shiga taitayin su don su yi abubuwan da zai dace da zaman lafiya na ƙasa.

Ci gaban da aka samu na ilimin kimiyya ya sa a yanzu ba a buƙatar wani babban gini idan za a kafa gidan talbijin ko rediyo, ko a ɗakin ka ma sai ka gudanar da aikin, don haka yasa wasu mutane ba su san ma da wata doka ba idan sun tashi buɗe kafar yaɗa labarai musamman a ‘Social Media’.

To duk wanda ya yi wannan ai ya yi ganganci, saboda akwai wata magana da masu gudanar da Shari’a su ke cewa, “rashin sanin shari’a ba hujja ba ce na ka sava wa shari’a,” don haka duk wanda ya yi hakan to ganganci ya yi, idan hukuma ta kama shi to gaskiya zai ɗanɗana kuɗar sa. Amma kuma ana samun haka ɗin, saboda ita wannan harkar ta jarida ta ta’allaƙa a kan mene ne sani na kimiyya ya kawo mata, kuma ta ya ya za kayi amfani da ita? Saboda harka ce ta kimiyya. Kuma duk ƙasashen da suka ci gaba da su ke kawo mana abubuwan suna nuna yadda za a samu sauƙi a harkar ne, da kuma yadda za a rage kashe kuɗi. Kamar a baya idan za mu ɗauki hoto a talbijin na NTA, sai kana da wanda zai ɗaukar maka hoto da wanda zai ɗaukar maka murya, ka ga sai kun yi aiki ku uku. Amma yanzu sai aka kawo sauxi da wayar ka ta hannu za ka iya ɗaukar hoto, za ka iya ɗaukar sauti. Kuma a cikin aljihun ka za ka saka, ka tafi duk in da ka ke so ka je. To ka ga an kawo sauqin wannan abin. Kuma wajen harkar yaɗa abin da ka ke so ka yaɗa, kamar yadda ka ce a baya sai an samar da ƙaton gini da manyan injina, amma a yanzu abu ɗan ƙarami za ka saka sai ka watsa abin zuwa tauraron ɗan’adam. Kuma idan ta ‘Internet’ ne za ka shiga kawai ka aika abin da ka ke son aikawa, to ka ga wannan ci gaban kimiyya ne ya kawo hakan. Amma dole in dai mutum ya na son ya yi wannan harka ta jarida yadda ta kamata kuma ta dace da doka ta ƙasa, dole ne ya ga cewa ya san mene ne buƙatar ƙasa a kan aikin sa.

A ɓangaren masu yawo neman labarai na ƙasa, sai ya zama da yawa kafafen yaɗa labarai sun mayar da masu aikin neman labari kamar mabarata. Sai ka ga wasu sun samar da kafar yaɗa labarai, rediyo ko jarida da talbijin, amma ba su cika ɗaukar nauyin masu neman labari ba, sai dai su tafi neman labari su san yadda za su yi su riƙe kan su.

To, akwai wata irin manufa da masu tafiyar da harkokin jaridu suka saka a zuciyar su, duk wani wanda ya ke son a yaɗa masa abin sa to ya biya. To wannan ne ya kawo cewa in an kawo labari ba za a duba a ga mene ne muhimancin wannan labarin ga jama’a ba, shin wanda za a bada labarin a kan sa ya biya? To ka ga daga wannan abu da aka shiga, sai ya zama masu gidajen jaridu suka nuna cewar idan suka tura mai nemo musu labari, ai ana ba shi kuɗi, amma a aljihun sa kawai ya ke sakawa, saboda haka me ya sa za su biya shi, bayan waɗanda ya ɗakko wa labarin sun biya shi, to abin da ya kawo wannan kenan, ni a nawa tunanin kenan, saboda mutum zai ga cewa idan ka tura mai neman labari kamar ofishin gwamna to ɗan abubuwan da a ke samu wataƙila sai a ga cewa ko Janar manaja ba zai samu dama kamar ta mai ɗakko labarin gidan gwamnati ba, saboda kowa ya ga gwamna za a ɗan bada abin hasafi, to sai ka ga ba a biyan masu neman labari, amma dai hakan ba dai-dai ba ne, saboda Idan har ka ɗauki mutum aiki to abin da zai ingata wannan aikin na sa shi ne biyan sa albashi.

Amma a yadda zai zama yana aiki babu albashi, to ka ga shi ma idan ya tashi ba labarin da zai kawo cigaban kamfanin zai kalla ba, wanda zai samu wani abu shi zai nema. To amma yawancin waɗanda su ke gudanar da aiki a kan haka, ba sa tunanin abin da zai kai ya dawo, har ya zo ya shafi aikin da su ke gudanarwa. Kuma ina ganin rashin hangen nesa ne. Idan ka san ba za ka iya ɗaukar nauyin ma’aikaci ba, to ban ga dalilin da zai sa ka ɗauke shi ba, ka ce ya je duk abin da ya samu shi ne albashin sa. Ni a nawa ra’ayin kenan.

To, a yanzu mene ne mafita?
To, mafita dai shi ne akwai doka da ta ce idan mutum zai buɗe gidan rediyo ko jarida da talbijin to zai shigar da manufar sa ga hukuma ita za ta tantance, ɗaya daga cikin abubuwan da a ke dubawa, shin wanda zai buɗe wannan kafar yaɗa labaran ya san ƙa’idar aikin jaridar da zai shiga? ko shi a kan sa ko kuma wasu daga cikin waɗanda za su mallaki wannan kafar yaɗa labarin, akwai masanin wannan harkar a cikin su? Idan har an tabbatar da cewar sun san harkar sai a ba sa dama, saboda duk wanda ya ke gudanar da wannan aikin ya san cewar akwai ƙa’idoji na tafiyar da aiki. Sannan kuma akwai ginshiƙin yadda a ke tafiyar da ayyukan wanda bai kamata ka karaya su ba, don haka wanda bai san wannan harkar ta yaɗa labarai ba, ka ga ba zai san yadda a ke gudanar da ita ba. Don haka a fara yin abu kan tafarkin ilimi kafin a ce an fara shi ne zai kawo ƙarshen matsalolin da a ke fuskanta a fagen aikin jarida.

To madalla, mun gode.
Nima na gode.