Rashin sha’awar iyali da dalilansu (5)

Daga BILKISU YUSUF ALI

Ci gaba daga makon da ya gabata kan abubuwan da suke sa sha’awa ga ma’aurata ko bayan babu ita ko kuma idan ta yi rauni.

Maganganu masu taushi:
Kissa da kisisina da maganganu masu taushi da daɗi da motsa sha’awa suna taimakawa ma’aurata kuma suna kusanto da sha’awa. Kowacce mace ita ta san yadda take tafiyar da mijinta da yadda take juyo da hankalinsa da zuciyarsa. Hatta a gun namiji shi ma ire-iren wannan lallashin da tausasa murya da maganganu mai daɗi suna taimaka masa wajen tada sha’awar matarsa har ta kai an samu abin da ake buƙata.

Motsa jiki:
Motsa jiki yana da matuƙar muhimmanci. A ƙalla a duk sati a samu sau huɗu ko biyar ko kuma kamar yadda jami’an lafiya suka faɗa. Daga mace har namiji suna buƙatar motsa jiki. Yawancin mata da maza da suka yi nauyi ko ƙiba kuma suna zaune ba sa motsa jiki suna fama da matsalolin sha’awa da rashin gamsar da juna. Don haka motsa jini ya zama wajibi a gun ma’aurata.

Motsawa:
Kyakkyawan motsi yayin da ake kusantar juna yana da amfani bai kamata ma’aurata musamman mace ta kwanta kamar dutse irin wannan ba ya taimaka wa Maigida bare har ya motsa sha’awa.

Tsarin kwanciya:
Akwai style kala-kala na kwanciya da ya kamata ma’aurata su san su sannan su gwada. Sau tari ma’aurata suna da zaɓi wasu sun sani wasu kuma ba su sani ba. Rashin gwada ire-iren wannan salo na kwanciya yana da tasiri kuma yana da kyau don akwai gundira a amfani da salo guda ɗaya don haka ma’aurata suke gwada salo daban-daban.

Gudanar da wasanni:
Hatta a addinin Musulunci ya yi umarni da a tura ɗan aike kafin a gudanar da mu’amalar aure. Ma’aurata musamman mata suna kuka da yadda mazajensu suke zuwa musu. Wasanni yana motsa sha’awa kuma a wannan wasannin ne miji kan gane ina ne makamar matarsa haka ita ma matar za ta gane ina ne mijinta ya fi so. Abu ma fi muhimmanci a irin wannan lokacin ma’aurata su cire duk wata damuwa su bayyanawa jinansu ra’ayinsu don ɗorewar aurensu.

Neman magani:
Idan har akwai wata larura da take kawo wannan matsalar ta rashin sha’awa yayin kusantar juna to wajibi ne a kawar da ita kafin a ga biyan buƙata. Ire-iren waɗannan larurori akwai ciwon sanyi da ciwon suga da hawan jini da nau’ikan basur da dai sauran larurori. Don haka yana da kyau ma’aurata su fara sanin yanayin rashin lafiyarsu kafin su fara yin magani.

Biyayya:
Abu na farko kuma na ƙarshe shi ne biyayya da ƙaunar juna duk sha’awa ba t a tasiri in har babu ƙauna da soyayyar juna da mutunta juna. Mace wajibi ta yi biyayya ga mijinta ta tausasa harshe ta laƙanci me yake so da bin da ba ya so. Sannan ki laƙanci lokacin da yake da sha’awar magana da lokacin da yake kyakkyawan yanayi da lokacin da ba ya son a dame shi. Idan ki ka kiyaye wa]annan abubuwa za ki mallaki sha’awar mijinki. Sannan shi ma maigida kana buƙatar ka ke mutunta matarka, ka ba ta duk haƙƙinta dai-dai gwargwado ka kyautatawa iyayenta wannan zai sa ta saki jiki, ita ma kuma kullum ta kasance cikin laluben hanyar da za ta faranta ma ka.

Ga mai neman ƙarin bayani ko tambaya kan wani abu da ya shafi lafiyar iyali yana iya aiko da tambayarsa ta hanyar wannan lambar 08039475191 ko ta shafina mai suna Ilham Special Care And Treatment.