Fasahar marubuta waƙoƙin Hausa

Waƙa: WAƘA
Tare da KHALID IMAM DA AMINU LADAN ALA

Da karanbani da naci,
Yaro kan koyi keke,
Wataran ko sai ya tuƙa
Babur mota da jirgi.

Dagiya naci da koyo,
Mai waƙa ke buƙata,
Da azanci har zalaƙa,
Da harshe mai balaga.

Ƙafiya kuwa in kana so,
Sassaƙa du a baiti,
Waƙa na ƙara zaƙi,
In akwai hikima azanci.

Waƙa tamkar kitso ce,
Sai da tsifa har da taza,
Kafin a kitsa a zana,
Cikin harshe na Hausa.

Ɗangon waƙa mu lura,
Yana da awo ma’auni,
Muryar waƙa aboki,
Saita ta ake a rera.

Waƙa tilas a auna,
Mai rerawa ya karya,
Muryarsa da kyau a waƙe,
Cikin rauji ya rera.

Ko makaho na rabewa,
Hanyar jirgi da mota,
Haka ma wawa da gaula,
Sun san mata ta aure.

Haka ma sauti na waƙa,
Ya sha bamban da zance,
Waƙa da salo da jigo,
Ake gina baitukanta.

Waƙa tamkar budurwa,
Kwalliya da adon jikinta,
Su ke sawa ta haska,
Ƙauna daraja ta samu.

Ta kere sa’a a birni,
Har ƙauye du a so ta,
Zuciyar jama’a ta sace,
A so ta ana ta shauƙi.

Waƙa tuni na fahimta,
Teku ce ta kere kogi,
Kuma tabbas arzikinta,
Yana da yawa cikinta.

Ni waƙa na fa gamsu,
Daji ce babu ƙyaure,
Bukka da gida sanina,
Su ne aka sawa ƙofa.

Sai mai nazari ya lura,
Don kar ya ɓace cikinsa,
Dajin waƙa da ɓauna,
Damisa giwa da zaki.

Haka ma in za mu duba,
Ma’adanai na nan cikinsa,
Da gwal da tama a jibge,
Zo mu tona sai mu dace.
© Khalid Imam

TA’ALIƘIN WAƘA
Haka za waƙa ta Hausa,
Fari ɗan ba kan ka ɗissa,
Basmala aka so ka dosa,
ko da larabci da Hausa,

Ai musamman ta rubutu,
Wacce ke wa zubin rubutu,
A yi rubutu a yi karatu,
Duka cikin tsari na sautu.

An ka ce da akwai ma’au nai,
Baharai da kari ma’au nai,
har ƙafafu ban ma’au nai,
Duka da su kuma ta yi mazau nai,

In ka ɗau waraƙa takarda,
Sai kace jigon Jarida,
Kai nufin saƙo ka ida,
Ƙarkashin waƙa kasida.

Fari jigo ne a farko,
In ka ɗauke basmala ko,
Sai ware jigo na saƙo,
Ɗai-da-ɗai ƙoƙo da ƙoƙo,

Acikinta zubi da tsari,
Kwai styele masu tsari,
Tsara baiticin a tsari,
Har zubi na ɗiya a tsari.

Har wa yau a salo na ƙaye,
Ban zubi tsari na ƙaye,
Sai a ɗunguma ba tsumaye,
Babu binbini da maye.

Kan Salo nake dai na harshe,
Ga Salon Sarrafa harshe,
Ga salo ko na saɓi zarce,
Gangara ka saɓa ka zarce.

Kuma cikin Casa ta baiti,
har da rauji ma a sauti,
Mai hawa sauka da Sauti,
Zaka jero duka a baiti.

Kana kwai zaɓe na kalma,
Ba a halin ƙarma ƙarma,
Sai da runbu nata kalma,
Gwargwadon dai taka himma,

Kar na zarme gun bayani,
Nai Uwa da makarɓiya ni,
Ta’aliki kada ya jani,
Na yi karambani na nuni.

Kai abokina ka jini,
Ga shi nai ƙari da nuni,
Shehu khalid wanga nuni,
Zai yi amfani gareni
@Aminu_alan_waqa

TA’ALIƘIN WAƘA 2

Haka nan yake ɗan Imamu,
Marubuci na garinmu,
Al-katibu sha’irinmu,
Tirmin danya ka ɗauka,

Bana shakka akan ka,
haka nan Alƙallaminka,
haka za ‘yancin ga naka,
Maraki kake babu doka.

Wannan tsarin misali,
Da ka yi shi bisa dalili,
Duk mai nazari ya kalli,
Sharhin ka akan ta doka.

Ya san tabban hakiƙa,
Ka san waƙa a doka,
kuma ma ka gane kanka,
Bisa ‘yancin Walwalarka.

Sai dai khalid Imamu,
Ita dai waƙar ga tamu,
Harshen hausar garinmu,
Larabci ya yi damƙa.

Nason deenin ga namu,
Wan deenil Islamu,
Yai tasiri gare mu,
Har ya yi kama da doka.

Sai gogayyar ga tamu,
Da masu zuwa garinmu,
Don bunƙasa garinmu,
Sun wa harshenmu tamka.

Na san ka san da wannan,
Dukkan harshen ƙasar nan,
Da bashi aro na wannan,
Baya kai tasa doka.

Kwai tasiri cikin mu,
Don addinin ga namu,
Ga kau huldar garinmu,
Ta saye da sayar a baka.

Ko da wannan rubutu,
Aro shi mukai karatu,
Mu da ba ma karatu,
Sai talifi zubin ka.

Amma yau ga rubutu,
Mai sadarwa ga karatu,
Bisa dokokin Rubutu,
Ba a yi da Molonka.
@Alan waƙa

AMSAR TA’ALIƘIN WA’ƘA

Nuninka kwarai Aminu,
Alan waƙa da sannu,
Na fahimta har da kanu,
Don fahimta na da fuska.

Fuska ta zubi da tsari,
Dawa masara fa gari,
In za a nuƙa da sauri,
Sai mai himma ya taka.

Gaskiya ka faɗi sani na,
Sai dai kuma ni a guna,
Waƙa ka kula gwanina,
Gona ce ban da shakka.

Wani gona tai da girma,
Shuka sai ya yi yamma,
Bai yin shara ta noma,
Sai ya watsa iri ya taka.

Wani ko noma ta rani,
Yake himma da nuni,
Cewa a yi babu rauni,
Bai jira noma da marka.

In manomi na da ‘yanci?
Allah ya ba shi naci,
Juriya ga haziƙanci,
Yai noma har da kaka.

Shi mawaƙi nasa ‘yanci,
Wa ya toshe nasa hanci,
Yai wa waƙa alamci,
Siga tsari da girka.

Ni ban rigima da tsari,
Domin kuwa ban da zari,
Kuma ban fama da yari,
Mari da mari da maka.

Ashe ko ina da dama,
Fura nono na dama,
Na sha ba na ladama,
Adabi ‘yanci ya ba ka.
© Khalid Imam