Sarakuna sun haɗa ƙarfi da Gwamnatin Tarayya kan ilmantar da yara a Argungu

Spread the love

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR, Birnin Kebbi

Gwamnatin Tarayya ta sanya hannu tsakaninta da Sarakunan gargajiya, akan wata yarjejeniya wadda za ta mai da yaran da basu a makaranta su koma makaranta su nemi ilmi.

An dai sanya hannu ne a garin Argungu tare da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar da Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera da kuma muƙaddashin sakataren zartarwa na hukumar Ilmi bai ɗaya mai Kula da Ilmin firamare da na
sakandare, (UBEC), Dr. Abdulrazaq Akinyele, wanda ya wakilci sakatariyar zartarwa ta hukumar.

Ita dai hukumar kula da Ilmin Firamare da na Sakandare, (UBEC), tare da haɗin gwiwa da gidauniyar Sultan mai manufar wanzar da zaman lafiya da raya al’umma, suka ɓullo da wannan shirin da zai ƙarfafa aiki tare wurin haɓɓaka Ilmin firamare da na sakandare.

Wannan hangen-nesa, wani muhimmin ginshiƙin ne na inganta ilmin firamare da na sakandare ta hanyar amfani da Sarakuna da kuma Shugabannin Addini, su shiga cikin shirin tsundum, domin samun nasarar shirin.

Wannan tsarin ya kawo fahimtar juna tsakanin gwamnati da mazauna karkara, wanda a yanzu yake gudana a jihohi guda hudu da suka ƙunshi Adamawa da Katsina da Sokoto da kuma Osun.

A lokacin rattaɓa hannun, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya bada tabbacin cewar sarakuna sun tashi tsaye wurin rage barace-baracen yara dake akan tituna, da nufin mayar da su makaranta a koyar da su Ilmin boko da na addini.

Ya ce Muslunci bai amince da barace-barace ba, saboda haka za su yi namijin ƙoƙari su sanya irin wadannan yara makarantun zamani.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya yi tambihi ga masu kudi ko hali, da su nuna jin-ƙai ga marayu, yana mai cewar akwai daruruwan marayu da ke gararamba akan tituna, kuma mafi yawansu, wadanda aka kashe ma iyaye ne, sanadiyyar ta’addanci da hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa wasu garuruwa.

Sarkin Musulmi ya gode ma gwamnatin Jihar Kebbi da kuma Gwamna Nasir Idris na daukar mallakin Gidan Marayu da ke Argungu, da nufin yaran da ke ciki su rika samun kulawar da ta inganta da kuma sanya su akan turba mafi amfani.

Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar ya shaida ma taron cewar, jama’a su yawaita addu’a, sannan kuma sarakuna sun fi kowa buƙatar addu’a a ƙasarnan, saboda muhimmin nauyin da ke akan kafadarsu.

Ya ci gaba da cewar, a wanzar da yi ma shugabannin Najeriya addu’oin alkhairi na samun nasarar mulki da kuma inganta rayuwar al’umma.

Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida wanda ya wakilci Gwamna Nasir Idris, shine aka damka ma Gidan Marayun wanda a yanzu ya koma mallakin gwamnatin Jihar Kebbi da kuma kulawa da shi.

Ita kuma uwargidan gwamnan jihar, (First Lady), Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, a karkashin Kungiyarta mai suna ‘NASARA Foundation’ tare kuma da taimakawan hadin gwuiwa daga Hukumar Kula da Ilmin Firamare da na Sakandare ta Ƙasa, (UBEC), da kuma Gidauniyar Sultan, sun baiwa Makarantun Allo na Qur’ani su 150, da aka zabo daga Masarautu hudu na Jihar Kebbi, gudunmawar kayayyakin sana’oi.

Kayayyakin sun haɗa da na ɗinkin-tela da sarrafa takalma da kuma sana’ar kafinta da za’a koyar ma yaran, domin dogaro da kai da kuma samun kudaden gudanar da rayuwar yau-da-kullum.

Shi kuma Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Sama’ila Muhammadu Mera, ya godema Hajiya Zainab Nasare dangane da yadda a kowane wata, tana baiwa gidan marayun da ke Argungu, Naira miliyan ɗaya kyauta, babu fa-shi, domin kulawa da su.

Sarkin Kabin Argungu ya yi bayanin cewar wani bawan Allah Attajiri, wanda bai son a ayyana sunansa, ya gina gidan marayun ya bayar kyauta ga al’umma, wanda a yanzu, gwamnatin Gwamna Nasir Idris ta karɓi mallakin sa da kuma kulawa da tarbiyyar marayun da ke ciki.

By ukarofi

Leave a Reply