Sarki Sanusi ya jagoranci sallar jana’izar babban ɗan tsohon Sarkin Kano, Abdullahi Bayero

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Laraba ce aka gudanar da sallar jana’izar Alhaji Idris Bayero, Hakimin Bichi kuma Barden Kano wanda ɗa ne ga marigayi Sarkin Kano Abdullahi Bayero da ya mulki Kano a tsakanin 1926 da 1953.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya jagoranci sallar tare da ɗarurwan mutane a Ƙofar Kudu.

Da farko, an ɗora wa Alhaji Idris Bayero rawanin matsayin Darman Kano kuma Hakimin Rimin Gado a shekarar 1990 ƙarƙashin jagorancin yayansa marigayi Sarki Ado Bayero (1963-2014).

A 1992 aka ƙara masa matsayi zuwa Ɗan Buram sannan dags baya kuma ya zama Barde kuma aka sauya masa waje zuwa Bichi a matsayin Hakimi.

Sarkin ya rayu da mata ɗaya da ƴaƴa 11 da jikoki da dama kuma ya rasu ya na da shekaru 90 a duniya.

By Babaji