DAGA JOHN D. WADA, a Lafiya
Wani basaaraken gargajiya mai suna Amos Poubinafa wato sarkin wani gari da ake kira Tungbbo da ke ƙaramar hukumar Sagbama ta jihar Bayelsa a yanzu haka yana kwanciya ne a cikin motarsa sakamakon kora da wata mummunar ambaliya ta yi masa daga fadar sa.
Wakilin mu da ya ziyarci sarkin a cikin sabuwar fadar na sa dake cikin motarsa, ya samu ganawa da shi akan bala’in da ya rutsa da shi inda ya bayyana alhininsa cewa “Ka ga kamar yadda kake gani, yau kimanin makonni biyu kenan da nake kwanciya da sauran harkokin rayuwata anan cikin motata kirar Toyota Sienna.
“Ambaliyar kamar yadda kake gani ya kai tsayin gwiwa na a yanzu kuma hakan yasa ba a iya zama a fadar tawa.” Cewar basaraken wanda har ila yau tsohon jami’in rundunar sojan ruwa ne wato retired naval officcr kenan a turance.
Sarkin ya cigaba da bayyana cewa “A halin yanzu motar nan ce kaɗai mafakata don ambaliyar ta riga ta mamaye duka ginin fadar tawa kuma babu wajen kwanciya a ciki.
“Tuni dai iyalaina suka yi ƙaura daga nan zuwa babban birnin Yenagoa sakamakon bala’in ambaliyar, ko ince jarabar ambaliyar. Yanzu dai na yanke shawarar cigaba da rayuwar fadarcina a cikin motar nan ne don bai kamata ace a matsayi na na shugaba, ubangari kuma kaftin na jirgin ruwan nan a wannan lamari in bar al’umma ta inje wai ina neman mafaka a waje ba. Kaji mataki dana ɗauka ma kai na kenan a kan lamarin nan.
“Kuma a irin horo na musamman dana samu a matsayin tsohon sojan ruwa, bai dace in gudu in kyale sauran abokan aikina matuƙin jirgin da nake jagora ba. Maimakon haka ni yakamata in tsaya har ƙarshe.” Inji shi.
Mai martaba sarkin na Tungbbo, Amos Poubinafa har ila yau ya bayyana wa wakilinmu cewa wannan ba shine karon farko da yake fuskantar lamarin ambaliya irin wannan ba don hakan a cewarsa, hakan ya faru da shi a shekarar 2012 da 2022 kuma a duka lokutan kamar yanzu bai yi watsi da al’ummarsa yaje ya nemi mafaka a wani waje daban ba.
Daganan sai yayi roƙo na musamman ga hukuma da ke ba da tallafin gaggawa wato National Emergency Management Agency a turance ta jihar Bayelsa din da sauran masu hannu da shuni su taimaka wa duka waɗanda lamarin ya shafa a wannan garin na Tungbbo don rage musu asara da suke yi a kullum da kuma samun walwala.
Ya kuma yi amfani da damar inda yayi kira na musamman ga gwamnatoti a duka matakai musamman ta tarayya su riƙa gina matattarar ruwa irin na zamani da gadoji da sauran su musamman don rage ƙarfin ruwan manyan kogunan nan biyu wato na Neja dana Benuwai da yace su suka fi jawo wannan manyan ambaliya a yankin nasa dama wasu sassan ƙasar nan baki ɗaya.
Ƙarin binciken wakilinmu akan tarihin basaraken dai ya gano cewa bayan yayi ritaya daga aikin sojan ruwa a matsayin babban kwamanda a shekarar 2002 ne sai daga bisani ya samu sarautar sarkin yankin nasa.
