Shaye-shaye ya sa na rasa aiki a kamfanin mai — Wani ɗan Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wani ɗan Nijeriya mai suna Abraham ya bayyana yadda shaye-shayen miyagun ƙwayoyi suka janyo masa rasa aikinsa a wani kamfanin mai, suka lalata dangantakarsa da iyalansa da abokansa, tare da jefa kusan shekaru 10 na rayuwarsa cikin asara.

Abraham, wanda a yanzu yake kan hanyar murmurewa daga jarrabar miyagun ƙwayoyi, ya bayyana irin abubuwan da ya fuskanta a shirin NarcoTales S4 E8, wanda aka watsa a tashar YouTube ta Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ranar Juma’a.

A cewarsa, ya fara fahimtar girman illar da shaye-shayen suka yi masa ne bayan da ya rasa aikinsa a wani kamfanin mai sakamakon warin jikinsa da ya kasance yana damun abokan aikinsa.

Abraham ya ce, a duk lokacin da ya shiga ofis, abokan aikinsa kan buɗe na’urar sanyaya iska da tagogi, tare da fesa turare cikin ofishin domin rage warin.

“Lokacin da na samu aikin, an ba ni damar yin aiki a wani kamfanin mai. Na taɓa cewa wannan kamfani ne da aka yi min alƙawarin zan samu aiki a cikinsa. Aikin ma ya kasance ya fi abin da nake nema.

“Amma mutane suka ci gaba da ƙorafin cewa jikina yana fitar da wari mai tsanani. A mafi yawan lokuta idan na shiga ofis, sai su kunna AC a buɗe tagogi, su riƙa fesa abin ƙamshi. Ban iya wuce wasu ’yan watanni a aikin ba. Dole suka sallame ni zuwa hutun jinya,” inji shi.

Abraham ya ce, rasa aikin ya sa ya fahimci cewa lokaci ya yi da zai fuskanci matsalar dogaro da miyagun ƙwayoyi da ke addabarsa.

Ya ce, a wannan lokacin ne kuma ya gane cewa ciwon da ya sa ya fara amfani da ƙwayoyin tun farko ya daina damunsa, amma har yanzu yana ci gaba da amfani da su saboda tsananin sha’awa da jarraba.

“Na fahimci cewa ciwon da ya sa na fara amfani da su tun farko, ba na jin shi kuma. Amma duk da haka, ina ci gaba da shan ƙwayoyin ne saboda sha’awa. Da zarar sha’awar ta taso, sai kawai na garzaya gare su. Ya zama kamar abin da jikina ke yi kai tsaye,” inji shi.

Ya ce, jarrabar ta shafi kusan dukkanin sassan rayuwarsa, ciki har da kuɗinsa, lafiyarsa, aikinsa da kuma dangantakarsa da sauran mutane.

Abraham ya ce, matsalar ta kuma shafi iyayensa, inda a lokacin da mahaifiyarsa ke ƙoƙarin taimaka masa, mahaifinsa da mahaifiyarsa suka rabu.

“A lokacin da nake fama da jarabar, mahaifiyata tana ƙoƙarin taimaka min, amma daga ƙarshe ita da mahaifina suka rabu. Wannan ya nuna cewa ba ni kaɗai abin ya shafa ba, har da iyalina baki ɗaya,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa duk da cewa yanzu ya murmure daga jarrabar, dangantakarsa da ’yan uwansa ta yi tsananin rauni sakamakon shekarun da suka shafe suna fama da matsalar.

“’Yan uwana yanzu, duk da cewa na murmure, saboda matsin da muka sha tsawon shekarun da nake cikin jaraba, sai muka ji kamar ba mu san juna ba. Wannan kusancin da ke tsakaninmu ya gushe,” inji shi.

Sai dai Abraham ya ce babban abin da ya yi asara a shekarun da ya yi yana cikin jarraba shi ne lokaci.

Ya ce ya rasa kusan shekaru 10 na rayuwarsa, inda a wannan lokacin ya kamata ya kasance yana aiki, tara kuɗi, yin aure da kuma gudanar da rayuwa mai kyau.

“Na rasa kusan shekaru 10 na rayuwata saboda wannan matsala. Me ya sa zan rasa wannan kyakkyawar rayuwar da ya kamata in kasance ina yi? Samun aiki, yin aure da sauran abubuwan da ke kawo kyakkyawar rayuwa. Na rasa waɗannan damammaki,” inji shi.

Abraham ya bayyana cewa ya kamu da jarrabar ne a tsakiyar shekarunsa na 20, kuma bai fahimci yadda rayuwa take ba tare da jin daɗin da miyagun ƙwayoyin ke ba shi ba, har sai da ya shiga shekarunsa na 30.

Ya ce, ko da yake mutum na iya rasa kuɗi ya sake samun wani, ba zai iya dawo da lokacin da ya ɓata ba.

“Da na iya tara kuɗi, amma idan ka rasa kuɗi za ka iya sake samun su. Amma lokaci abu ne da ba za ka iya dawo da shi ba. Ba za ka iya dawo da lokaci ba,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa yawan allurar da ya yi amfani da ita tsawon shekaru ya bar masa tabo a jikinsa, tare da janyo masa matsalar tafiya da kuma rashin iya yin wasu abubuwan da yake jin daɗinsu a baya.

“Ina ganin abin da ya fi damuna shi ne tabon da ke jikina. Har yanzu idan na farka na kalli jikina, sai na ji kamar mafarki nake yi,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, “Sakamakon sanin cewa ba zan iya sake gudu ba yana damuna. A da ina matuƙar son rawa, amma yanzu hakan ya tafi. Na zama mai nakasa a wani ɓangare na jikina, kuma duk lokacin da zan yi tafiya, dole in riƙa ɗingishi.”

Abraham ya ce, a lokuta da dama yana sanya dogayen kaya da safa domin ya ɓoye tabon da ke jikinsa, saboda ba ya jin daɗin fallasa su a gaban jama’a.

Ya kuma ba da labarin wasu munanan halayen da ya tsinci kansa a ciki a lokacin da jarrabar ta tsananta, ciki har da satar kuɗi daga wajen mahaifiyarsa da kuma roƙon baƙi kuɗi domin ya sayi miyagun ƙwayoyi.

“Ban taɓa tunanin zan iya yin sata ba. Amma na sace wa mahaifiyata lokacin da jarabar ta tsananta sosai,” inji shi.

Ya kuma bayyana cewa ya taɓa yunƙurin kashe kansa har sau uku, sannan ya shiga halin dogaro da baƙin mutane domin samun kuɗin da zai saya miyagun ƙwayoyi.

Ya ce ya kan yi yawo a tituna yana roƙon mutane kuɗi, daga shago zuwa shago, domin ya samu abin da zai saya.

Sai dai Abraham ya ce samun damar murmurewa daga jarrabar ya samu ne saboda mutanen da suka ci gaba da yarda da shi tare da ba shi goyon baya, musamman limamin cocinsa da sauran ’yan cocin, baya ga taimakon ƙwararru.

Ya ce ƙoƙarinsa na farko na zuwa cibiyar gyaran jaraba ya ɗauki kusan wata guda, amma makonni kaɗan bayan ya fita sai ya koma amfani da miyagun ƙwayoyin.

By ukarofi

Leave a Reply