Marubuci:JIBRIN YUSUF KAILA
A kowanne zamani da al’umma, akwai makusantan hanyoyin da ake bi don bayyana tunani, gyara rayuwa da fahimtar juna. ɗaya daga cikin waɗannan hanyoyi kuwa ita ce rubutu. Arewacin Najeriya ya shahara da marubuta da dama, amma abin takaici, har yanzu ana kallon mace marubuciya da wani irin ido na zargi, wulaƙanci ko kuma tsoro. A wannan muƙala, zan yi sharhin matsin lamba da tozarci da ake yi wa mata marubuta a Arewa da yankin Hausawa da fulani har da ƙasashen Hausawa kamar su Niger, Camero, Chadi da sauran yanki da ake jin Hausawa. Da kuma bayyana mahimmancin aure da mace marubuciya, da kuma yadda al’umma ke buƙatar sauyawa wajen fahimtar wannan matsayi.
Ina cike da mamaki Irin yadda na ga mata suke fuskantar ƙalubale, a lokacin da suka bayyana cewa su za su zama marubuta, ina da tarin mata da suke mun magana akan ƙalubale da suke fuskanta da zarar sun bayyana cewa suna son su zama marubuta, har yanzu yankin mu na Arewa suna da ƙaranci fahintar shin kansa rubutu da kuma masu rubutu. Mata da yawa an daƙile mu su burinsu da yawan mata da suka shahara Arewa sun fuskanci ƙalubale, musamman wanda suka yi nasara na zama gwarzaye irin su kamar ta BBC Hausa ko Gasar Gusau Institute. Kawai na ci ne da juriya ya sa suka kao gaci nan, kuma abin da zai baka mamaki shi ne idan marubuci ya yi nasara sai ka ga masu nuna adawa su suke nuna alfahari da gadara…
Lokaci ya yi da masu adawa da yin rubuce-rubucce da su farka su yi nazari da bincike akan me ye rubutu da marubuta da gudunmawar su. Ina da tarin labarai da wasu mata ke faɗa mun kan irin ƙalubale da suke fuskanta, shi ya sa rubutuna ya fi karkata akan sababbin marubuta. Akwai tarin tulun masu burin zama marubuta wanda suke da hiikima da basira da al’umma za su ƙaru da rubuce-rubuce su kuma za su amfana amma rashin ƙarfin gwiwa agun makusantasu walau miji, iyaye, yayu da samarin da zasu auren da sauransu su ke daƙile su.
1. Wasu Dalilan da ke hana mace zama marubuciya a Arewacin Najeriya
a) ɗabi’ar tsoro da al’adun gargajiya
A al’ummar Hausa da dama, mace tana da matuƙar nauyi a matsayin matar aure, uwa ko ’yar gida. Wannan ya sa wani lokaci ana ganin duk wani yunƙuri da mace ke yi wanda ya wuce iyakar gida ko makaranta, musamman rubuce-rubuce na adabi ko ra’ayi, a matsayin “ɓallewa daga tarbiyya”.
b) Zargin lalata tarbiyya
Wasu sukan ce marubuciya tana amfani da rubutunta wajen fallasa sirrin iyali, ko kuma tana rubuce abubuwan da za su sa ta zama ba ta da kunya. A ce mace ta rubuta soyayya, ko magana mai zurfi game da zamantakewar aure, nan da nan za a zarge ta da rashin ladabi ko neman hankali.
c) Tsoron shahara da girma fiye da miji
Wani abin kunya da ke damun maza da dama shi ne, mace marubuciya na iya samun suna fiye da mijinta – ta wallafa littafi, ta sami karramawa, ta yi jawabi a gaban jama’a. Wannan yana haddasa ƙiyayya, tsoro ko har ma da kin aure.
d) Tsangwama daga gida ko iyaye
Iyaye da dama ba sa goyon bayan diyarsu ta shiga harkar rubutu, musamman idan hakan zai sa ta fara hulɗa da jama’a da yawa ko bayyana a kafafen sada zumunta. Wannan tsoro yana hana ‘yan mata dama mai kyau.
2. Haushin da ke tattare da wannan tsangwama
Ba laifi ba ne mace ta iya tunani, ta rubuta ra’ayinta, ta wallafa littafi ko ta shahara da hikima. Idan ana yi wa mace marubuciya kallo na wulaƙanci, to wannan ya nuna cewa har yanzu ba a karɓi gaskiyar cewa mace na da cikakken tunani da fasaha irin ta namiji ba. Wannan kallo yana rage girman ci gaban al’umma.
Muna cikin ƙarni na 21, amma har yanzu ana ganin mace marubuciya a matsayin barazana. Wannan abin takaici ne. Domin a lokacin da duniya ke ƙarfafa mata su tsaya da kafafunsu, mu kuma muna kulle su da zargin “ta yi yawa”, “ba za ta yi aure ba”, “za ta lalace”, da makamantan haka.
3. Fa’idodin auren mace marubuciya
Idan muka duba da adalci, mace marubuciya tana da fa’idodi da dama ga mijinta da al’umma:
a) Mace mai ilimi da hangen nesa
Mace marubuciya yawanci mai ilimi ce, mai karatu, mai basira. Wannan yana taimakawa wajen tsara rayuwar aure mai tsafta da fahimta. Zata iya ba da shawara, fahimtar mijinta da ƙarfafa shi cikin matsaloli.
b) Mai iya rubuta tarihin gida da dangantaka
Mace marubuciya zata iya rubuta tarihin rayuwarsu da mijinta, ta faɗakar da duniya da abin da za a koya daga auren su. Wannan wata kyauta ce da ba kowa ke da ita ba.
c) Garkuwa ce ga mijinta
Tunda mace marubuciya tana da fahimta, tana iya kare sunan mijinta da mutuncinsa a cikin rubuce-rubucenta, ko ma ta ba shi kariya daga mummunan fahimta daga jama’a.
d) Taimako cikin harkokin rayuwa
Mace marubuciya na iya samun kuɗin shiga ta hanyar wallafa littattafai, buga rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta, ko ma bada horo. Wannan zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin gida.
4. Abin da al’umma ke buƙatar yi
A bar tsangwama da zargin mace marubuciya: Idan namiji zai rubuta ra’ayinsa ba tare da zargi ba, to dole a bar mace ma ta rubuta nata cikin ‘yanci.
A goyi bayan mace marubuciya: Iyaye, malamai da mazaje su ɗauki mace marubuciya a matsayin jaruma, ba barazana ba.
A canza tunanin cewa mace marubuciya ba ta da tarbiyya: Domin akwai mata marubuta da suka fi mazan tarbiyya da kamun kai
Ba laifi ba ne mace ta zama marubuciya. Kuma ba laifi ba ne a auri mace marubuciya. Abin da ya kamata shi ne a fahimci cewa rubutu baiwa ce daga Allah, kuma idan mace ta ci gajiyarsa, to kamata ya yi a goya mata baya, a ba ta damar haskakawa.
Jibrin Yusuf Kaila marubuci ne da ke sharhi kan harkokin adabi, ya aiko wannan rubutun ne daga Jihar Jigawa.
