‘Yan sanda sun kama ɗan shekara 30 da ya kashe mahaifiyarsa a Jigawa

Spread the love

Daga USMAN KAROFI a Abuja

Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta kama wani matashi mai shekaru 30 da haihuwa bisa zargin kashe mahaifiyarsa da hannunsa a unguwar Dantanoma, ƙaramar hukumar Gumel ta jihar. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 8 na dare a ranar Lahadi, 29 ga watan Yuni, 2025, inda hukumar ‘yan sanda ta Gumel ta samu rahoton kai tsaye kan tashin hankalin tsakanin mahaifiyar da ɗanta.

Bayan isa wurin da lamarin ya faru, jami’an tsaro sun gano cewa Hussaini Abubakar ya kai wa mahaifiyarsa, Dahara Mu’azu mai shekaru 75, hari ta hanyar dukan kanta da tubalin ƙasa har sai da ta fadi cikin jini.

An garzaya da ita zuwa Asibitin Gwamnati na Gumel, inda aka tabbatar da mutuwarta a ranar Litinin, 30 ga Yuni, daga bakin wani likita da ke bakin aiki.

Ana ci gaba da tsare wanda ake zargi a hannun ‘yan sanda, kuma ya na taimakawa wajen bincike. Rundunar ta bayyana cewa da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP AT Abdullahi, ya bayyana lamarin a matsayin abin kunya, rashin imani da kuma aiki ba tare da tausayi ba.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta yi kira ga jama’a da su riƙa kai rahoton duk wani alamar taɓin hankali ko tashin hankali na cikin gida ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko shugabannin al’umma, domin hana aukuwar irin wannan mummunan lamari. Rundunar ta kuma jaddada ƙudirin ta na kare rayuka da tabbatar da doka da oda a faɗin jihar.

By ukarofi