Marubuta Hausa da fasahar AI

Spread the love

“Rubutun da ba shi da rai ba zai iya taɓo zuciyar mai karatu ba”

Daga AISHA ASAS 

A zamanin da duniya ke cike da saurin cigaba, fasaha, da kwaikwayon halittu, ya zama wani canji da ya samu matuƙar tasiri a rayuwar wannan zamani, wanda ya kai mutane da dama suka dogara kacokam kan fasahar, saidai hakan bai hana kalmar mutum ƙara samun daraja fiye da dukan wani cigaban kimiya da aka sani ba, domin dai ba yadda za a yi bawa ya fi wanda ya halicce shi.

A shekarun baya, marubuta sun gamu da gagarumar barazana: sabuwar fasahar zamani ta AI, wato Artificial Intelligence. AI na nufin fasahar da ke bai wa kwamfuta, na’urori ko injuna ikon yin abubuwa kamar yadda ɗan adam ke yi da hankalinsa kamar su fahimta, tunani, yanke shawara, koyon abubuwa, da magana. Wadda a halin yanzu ta fara bayyana a matsayin sabon marubuciya. Ta fara wallafa littattafai, rubuta labarai, har ma ta fara samun karɓuwa a wuraren da marubuci ɗan adam ke kaiwa da ƙwarewa. Saidai abinda yake da tabbaci shi ne, duk rubutun da ba shi da rai ba zai iya taɓo zuciyar mai karatu ba. Injin ko na’ura na iya tsara kalma, amma ba zai iya bayyana bakin ciki ko kishiyar sa ba.

Tasirin AI ga marubutan gaskiya:

Rahotanni daga mujallar Wired da wasu fitattun kafafen watsa labarai sun bayyana yadda kamfanonin AI ke amfani da rubuce-rubucen marubuta ba tare da izini ba domin horar da injinansu. Ana ɗaukar ayyukan marubuta don samar da rubuce-rubuce rayayyu masu ɗauke da ababen da ɗan adam ke iya ji ko gani, da ita na’ura ba ta iya yin hakan. Wanda ta hanyar ba su horo da rubutun da mutum mai rai ya yi, zai taimaka wurin gyara kura-kuran da take yi, ya kuma sanar da su yadda za su misalta ababen da ɗan adam ke ji a matsayinsa na mutum. Sannan kuma su san yadda za su iya taɓo zukatan masu karatu.

Wasu na ganin ba wa AI damar nazartar littafan marubutan gaske zai taimaka wurin cigaban fasaha a duniya. Saidai abin tambayar anan, shin yin hakan adalci ne ga su marubutan da suka ƙirƙire rubutun daga ƙwaƙwalwarsu?

ƙungiyoyin kare haƙƙin marubuta sun nuna damuwa, inda suka bayyana cewa daga 2006 zuwa 2022, ribar marubuta ta ragu da fiye da kashi 60.2%. Wasu gidajen wallafa kamar The Atlantic da Financial Times sun shiga yarjejeniya da kamfanonin AI, abin da wasu ke kallonsa tamkar sayar da fasaha ne ga mutum-mutumi. Sai dai jaridun New York Times da wasu gidajen wallafa sun ɗauki matakin kare marubuta, har da kai ƙara zuwa kotu.

Kamar yadda Hausawa ke cewa: “Wanda ya ce maka ya fi ka, tambaye shi abin da ya fi ka da shi. Duk wanda zai ce fasar AI ta fi ɗan adam, to tabbas bai karanci abin yadda ya kamata ma. Mutum ne ya haliccime na’ura don ta sawwaƙa ma shi ayyukan yau da kullum, don haka yana da ikon sa mata abinda yake da iko kansa ne kawai, wato ilimi da fasahar da yake da ita, amma ba shi da damar saka mata abinda ba shi ya ba wa kanshi ba, misali, injin bai san dalilin da ya sa kake kuka, balle ya bayyana shi da tausayi.

Ko AI ta san ƙimar rubutu?

Rubutu ba tarin kalmomi ba ne, amana ce daga zuciyar marubuci zuwa zuciyar mai karatu. Ba kawai don karatu ba, har ma don koyarwa, faɗakarwa da kuma koyi kan rayuwa. Na’ura ba za ta iya fahimtar damuwar da marubuci ke ciki ba. Ba za ta san irin wahalar da yake sha yayin da ya zauna cikin dare yana rubutu mai motsa zuciya ba.

Wannan dalili ne da ya sa fim ɗin ‘The Last Screenwriter’, wanda aka ce AI ta rubuta, aka soke shi a birnin Landan bayan masu kallo fiye da 200 sun nuna ƙin amincewa da saƙon da ke ciki, wanda suka fahimci sam ba shi da rai. Mutum yana buƙatar ganin kansa a cikin labari, ba a cikin lissafin algorithm ba.

Marubutan Hausa: Muryar da ke fuskantar barazana:

Ko da yake barazanar AI ta fi fitowa a ƙasashen yamma, kuma a can ne ta fi tasiri, saidai hakan ba yana nufin Hausa ba ta tsira ba. A Najeriya, musamman Arewa, inda harshen Hausa ke da ɗimbin masu karatu, marubutanmu na fuskantar matsaloli da dama: rashin daraja daga cikin gida da kuma mamayar fasahar waje.

Tarihin marubutan Hausa ya faro tun daga Abubakar Imam da Sa’adu Zungur zuwa fitattun marubuta irin su Balaraba Ramat Yakubu, Nazir Adam Salih, Hafsat Idris, Bilkisu Funtua da sauransu. Sun yi namijin ƙoƙari wajen raya al’ada da harshe ta hanyar rubuce-rubuce. Amma yau, da yawa daga cikinsu na neman shuɗewa da ransu, darajarsu ta yi ƙasa, ga uwa uba siyar da kalmominsu da ake yi a farashi mai ban tausayi.

Abin takaici, wasunsu na zaune za su ga kalamansu a manhajojin AI da ke ƙoƙarin rubuta ‘littafan soyayya’ cikin Hausa, duk da cewa babu ɗanɗano irin na malam Bahaushe, don haka tasirin su ba zai iya kai ga nasu ba, saidai kasancewar karɓuwar AI ta fi tasu, sai a zubar da su a je ga rubutun marar rai. Saidai bada jimawa ba hankalin mutane ya dawo kansu, sakamakon rashin gamsuwar da ke tattare da fasahar, domin AI na iya fassara, amma ba za ta iya ɗora wa kalma ɗanɗano ba. AI na iya rubuta baituka, amma ba ta san illar auren dole a garuruwanmu ba.

Wasu marubutan Hausa sun koma buga littattafansu da kansu, wasu na wallafa labaransu a kafafen sada zumunta, saidai abin tausayin, rubuce-rubucensu na tashi ne wajen ciyar da injinan AI gaba, ta hanyar koyar da su dabarun da shi marubucin ne kawai ya sani a matsayinsa na mutum, abin ƙarin takaici kuwa shi ne, babu wani neman izini, bare a yi zancen biyan lada ga wannan babban aiki da suke yi wa na’urorin zamani.

Ina mafita ga marubutan?

1. A kafa ƙungiyoyi masu kare haƙƙin marubutan Hausa daga amfani da ayyukansu ba tare da yardarsu ba.

2. A shirya taruka a manyan birane kamar Kano, Kaduna da Sokoto domin wayar da kai kan barazanar fasahar AI.

3. A farfaɗo da tsarin koyar da Hausa da rubuce-rubucen da ke ɗauke da al’adunmu.

4. A haɗa gwiwa da masana kimiyya domin gina hanyoyin kare rubuce-rubenmu daga mamayar fasahar waje.

Daga ƙarshe abin da ya kamata marubuta su yi riƙo da shi, rubutun ɗan adam na ɗauke da rai, tarihin ƙasa, da murya mai motsa hankali. Kada mu bar AI ta shafe sahihin rubuce-rubucen da suka gina tunaninmu da al’adunmu. Kada mu yarda da rugujewar muryarmu cikin lissafin marubuta da suka ba wa al’ummarsu gudunmawa da basirar da Allah ya ba su.

By ukarofi