Majalisar Dokokin Katsina ta buƙaci gwamnati ta ɗauki matakin inganta ilimi da lantarki

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hon Shu’aibu Bugawa mai wakiltar mazaɓar Mani ya gabatar da ƙudirin yana kira ga ɓangaren zartarwa da ya karɓi makarantar sakandare na al’umma da ke garin Magami domin mayar da ita ƙarƙashin kulawar gwamnati.

Ya ce hakan zai taimaka wajen inganta ilimi da samar da ƙarin guraben karatu ga ɗaliban yankin.

Shima dai Hon Abdulrahaman Saleh kiransu mai wakilan Rimi ya nemi gwamnatin jihar da ta gaggauta gyara da sauya kayan lantarki a ƙauyukan Kurabau,Masabo,Kadandani da Sabon Gari.

Ɗan majalisar ya bayyana cewar al’ummar yankin na fama da matsalar rashin wuta na tsawon lokaci wanda ya jefa masu ƙananan sana’o’i cikin babban matsala.

Haka ma Hon Mustapha Sani Bello na mazaɓar Mashi ya gabatar da ƙuduri na gina magudanan ruwa a gunduma 11 na ƙaramar hukumar Mashi domin magance matsalar ambaliya da taɓarɓarewar hanyoyi musamman a lokacin damina.

Majilisar ƙarƙashin jagorancin kakakin ta Rt Hon Nasiru Yahaya Daura ta amince da dukkan ƙudurorin sannan ta umurce akawun majalisar dokokin da ya aike wa ɓangaren zartarwa domin ɗaukar mataki.

By ukarofi