Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da katafaren shiri a ɓangaren kiwon lafiya

Spread the love


Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Shugaba Tinubu ya Ƙaddamar da Katafaren Shiri a ɓangaren kiwon lafiya da nufin kafa sabbin cibiyoyi goma na yaƙi da cutar Kansa tare da bai wa sama da ma’aikatan kiwon lafiya 120,000 sabbin horo.

A wani yunƙuri na inganta kiwon lafiya a Nijeriya,
Shugaba Tinubu ya Ƙaddamar da wani shiri na faɗaɗa harkokin kiwon lafiya, wanda ya haɗa da samar da sabbin cibiyoyin gano cututtuka guda 10 a shiyoyi shida na Nijeriya.

Shirin, wanda aka Ƙaddamar da shi tare da haɗin gwiwar hukumar kula da zuba jari ta Nijeriya (NSIA), na da nufin inganta hanyoyin kiwon lafiya, da bunƙasa tattalin arziki. Shirin, zai kuma sanya Nijeriya a sahun gaba cikin ƙasashe masu manyan cibiyoyin kula da lafiya a nahiyar Afrika.

Bugu da ƙari, za a samar da ƙarin horo ga ƙwararrun ma’aikatan kiwon lafiya har guda 120,000 don inganta ƙwarewarsu wajen bayar da kyakkyawar kulawa ga ‘yan Nijeriya a fannin lafiya.

By ukarofi