
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati, EFCC a wani karo ta sake tsare shugaban hukumar jigilar alhazan Nijeriya (NAHCON), Jalal Arabi tare da sakatarensa, Abdullahi Kontagora, sakamakon bincike da ta ke mu su na zargin sarrafa kuɗaɗen tallafin Alhazan shekarar 2024 da adadin su ya kai Naira biliyan 90 ba bisa ƙa’ida ba.
Rahotanni sun ce EFCC ta gano kuɗin Saudiya daga Arabi da wasu manyan jami’an NAHCON da adadinsu ya kai kimanin Riyal 314,098.
Binciken EFCC ya nuna cewa, a na zargin Arabi ya kimtsa biyan kan sa da wasu jami’an sama da kima daga kuɗin tallafin aikin hajjin.
Haka nan, wasu takardu daga EFCC sun bayyana adadin alawus na aikin hajjin da kowane jami’in NAHCON zai samu kamar haka; shugaba/CEO, Dala 4,250; kwamishinoni, $12,750; Sakatare, $3,845; Daraktoci da shugabannin ma’aikata, $15,300.
Saidai, hukumar ta ce Arabi da sauran jami’an sun karɓi abin da ya fi haka nesa-ba-kusa-ba.
An ruwaito cewa, Arabi ya karɓi Riyal 50,000 madadin 15,929. Haka nan, kwamishinoni uku sun karɓi Riyal 40,000 a madadin 15,929. Haka shima sakataren ya karɓi Riyal 30,000 madadin 14,336, sai Daraktoci da shugabannin ma’aikata da suka karɓi kwatankwacin haka a madadin 2,550.
A ranar 29 ga watan Yuli ne EFCC ta fara gudanar da bincike kan Arabi wanda bayan haka ne ta sako shi inda a makon da ya gabata ne kuma hukumar ICPC ta kama wasu jami’an NAHCON kan badaƙalar Naira biliyan 90 na tallafin aikin hajjin 2024.
