Shugaba Tinubu ya haďu da Peter Obi da Fayemi a Fadar Vatican

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

A ranar Lahadi ne Shugaba Bola Tinubu da ďan takarar Shugaban ƙasa a Jam’iyyar LP da tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi suka haďu a taron ķaddamar da Fafaroma na 14 a Birnin Rome.

An ruwaito cewa, Fayemi ne ya hango Shugaba Tinubu tare da sauran manyan ƙasashen duniya, inda ya nemi Obi da su je su yi masa gaisuwar ban-girma.

A yayin ganawar tasu ne manyan ƴan Nijeriyar suka yi raha a tsakanin su yayin da Fayemi ya ce wa Tinubu “Mista Shugaba maraba da zuwa cocinmu, sannan mun gode da ka amsa gayyatar Fafaroma.” Sai Tinubu ya ce masa, “Ni ne wanda zai marabce ka da Obi. Ni ne Shugaba tawagar Nijeriya.”

A kwanakin baya ne Sabon Fafaroman ya zabi Tinubu a matsayin ďaya daga cikin jagororin ƙasashen duniya da ya gayyata zuwa wajen taron kaddamarwar.

By Babaji