Daga GAMBO ISA a Abuja
Shugaban ƙaramar hukumar Bayo, Usman Balbaya Maidoki, ya yaba wa Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Baba Gana Umara Zulum, bisa jajircewarsa wajen kawo ci gaba da kuma tafiyar da gwamnati mai bai wa kowa dama a faɗin jihar.
A cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a Abuja kuma aka bai wa jaridar Blueprint Manhaja, Hon. Usman Balbaya Maidoki ya bayyana muhimman nasarorin da gwamnan ya samu a fannoni da suka haɗa da bunƙasa jarin ɗan Adam, noma da kiwo, ilimi, kiwon lafiya, tsaro da kuma samar da kayayyakin more rayuwa.
Shugaban ƙaramar Hukumar ya yaba da gyare-gyare da gina sabbin sakatariyoyin gwamnati na zamani, sanya fitilu masu amfani da hasken rana a tituna ciki har da na Bayo, da kuma faɗaɗa hanyoyin cikin gari da na tsakanin al’umma a sassa daban-daban. A cewarsa, waɗannan ayyuka sun inganta ayyukan gwamnati a matakin ƙasa da kuma ƙara kusantar da shugabanci ga al’umma.
Hon. Maidoki ya kuma yaba wa Gwamna Zulum kan gina gidan baƙi a Bayo, da kuma samar da magudanan ruwa da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana domin sauƙaƙa samun ruwan sha mai tsafta da kuma magance matsalolin sufuri a yankin.
Dangane da tsaro, shugaban ƙaramar hukumar ya jinjinawa gwamnan bisa ɗaukar matakai na gaggawa da suka haɗa da sayen kayan aikin tsaro, ci gaba da tallafa wa hukumomin tsaro da ƙungiyoyin sa-kai, gudanar da bitar tsaro akai-akai, da samar da ababen hawa tare da kula da su. Ya buƙaci al’umma da su ci gaba da zaman lafiya da ɗaukar alhakin bai ɗaya wajen yaƙi da ta’addanci.
A ɓangaren kiwon lafiya kuwa, ya yabawa gwamnatin bisa horas da ma’aikatan lafiya, inganta cibiyoyin kiwon lafiya, da gina asibitin zamani a Bayo tare da wasu cibiyoyin lafiya na matakin farko da ɗakunan shan magani a sassan jihar domin ƙara samun ingantaccen kiwon lafiya.
Da yake magana kan noma, Hon. Maidoki ya ƙarfafa gwiwar manoma da makiyaya da su yi amfani da shirye-shiryen gwamnati na tallafawa noma da kiwo, ciki har da rabon kayan noma, samar da wuraren kiwo da kuma ayyukan likitocin dabbobi. Ya bayyana Bayo a matsayin ɗaya daga cikin muhimman cibiyoyin noma a Arewa maso Gabas, tare da jaddada muhimmancin zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya domin ɗorewar ci gaba da zaman lafiya.
Shugaban ya kuma yaba da shirye-shiryen ƙarfafa matasa da gwamnatin Zulum ta ɓullo da su, ciki har da koyar da sana’o’i da shirye-shiryen koyon dabarun kasuwanci a Bayo da faɗin jihar, wanda ya ce zai kara bunƙasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi ga matasa.
Honourable Usman Balbaya Maidoki ya bayyana Gwamna Zulum a matsayin shugaba mai hangen nesa, wanda jarumtaka da tsayuwar dakan sa suka taimaka wajen magance matsalolin tsaro a jihar tare da inganta hadin gwiwar samar da kudaden tsaro domin yaki da ta’addanci.
A ƙarshe, ya buƙaci al’umma, shugabannin gargajiya, ma’aikatan gwamnati da na ƙananan hukumomi da su ci gaba da marawa shirye-shiryen gwamnati baya, su kasance masu riƙon amana a ayyukansu, tare da yi wa Jihar Borno da Nijeriya baki ɗaya addu’ar samun ci gaba mai ɗorewa.
