Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Argungu Alhaji Auwalu Danjimma (Sarkin Alhazzan Kabi. ) ya ja kunnen yan bangar siyasa kan cin zarafin mutane.
Alhaji Auwalu Danjimma ya yi wannan kiran ne a wani zama da ya yi da mambobin ƙungiyoyin siyasa da ke ƙarƙashin jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar mulki ta Argungu.
Ya ce daga yanzu ba sa son su ƙara jin wani ɗan goyon bayan su musamman yan bangar siyasa ya ci zarafin wani daga cikin shugabanni ko da kuwa ba shi ne ra’ayin sa ba.
An riga an kammala zaɓen fitar da gwani saboda haka yanzu an zama abu ɗaya.
Ya ƙara da cewa mallakar katin zaɓe duk ya fi wani zage-zage.
