Shugaban makarantar Unguwar Gano ya tunatar da ’yan majalisa alƙawarin tallafi

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Unguwar Gano da ke Yalwa, Malam Auwalu, ya tunatar da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar Hukumar Tarauni, Hon. Kabiru ɗahiru Sule, da shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Ahmad Muhammad Ibrahim Secure, alkawuran da suka yi na tallafa wa makarantar.

Malam Auwalu ya ce Hon. Kabiru ɗahiru Sule, wanda aka fi sani da ADS, ya yi alkawarin gina ɗakin jarabawa da masallaci a harabar makarantar, tare da bayar da kujeru 20. A cewarsa, daga baya ɗan majalisar ya ƙara yawan kujerun zuwa 50.

Ya bayyana cewa lokacin da shugabannin makarantar suka kai masa ziyara domin nuna godiya bayan halartar bikin yaye ɗaliban makarantar a shekarar 2025, ya kuma ba su allunan karatu na zamani, duk da cewa bai yi alkawarin bayar da su tun farko ba.

Malam Auwalu ya bayyana godiyarsa kan tallafin, amma ya ce makarantar na ci gaba da buƙatar kulawa da tallafi domin inganta ayyukanta.

Ya yi wannan bayani ne bayan kammala gasar Turanci tsakanin ɗaliban makarantun yankin, wadda aka gudanar ranar Larabar da ta gabata a ƙarƙashin taken Inter-School Spelling Bee.

Shugaban Hukumar Kula da Haƙƙin Masu Saye da Masu Sayarwa ta Jihar Kano (CPC), Dakta Ibrahim Garba Muhammad, ne ya ɗauki nauyin shirya gasar domin bunƙasa ilimi da ƙwarewar ɗalibai.

Haka kuma, Malam Auwalu ya yi kira ga shugaban ƙaramar Hukumar Tarauni, Hon. Ahmad Muhammad Ibrahim Secure, da ya cika alkawarin gina katanga tsakanin makarantar firamare da sakandaren Unguwar Gano.

Ya ce rashin katanga da ƙarancin azuzuwa na daga cikin matsalolin da makarantar ke fuskanta a halin yanzu.

Shugaban makarantar ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kano kan ƙoƙarinsa na bunƙasa ilimi, tare da gode wa sauran jami’an da suka halarci taron ko suka wakilci shugabanninsu.

Daga cikin waɗanda aka ambata akwai Babbar Sakatariya a Ma’aikatar Ayyuka na Musamman, Hajiya Uwani Ahmad Balarabe; babban sakataren Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (KSSSMB), Hon. Rabi’u Sale Gwarzo, wanda Daraktan Makarantun Kano, Malam Sani Haladu, ya wakilta; da Daraktan Ilimi na ƙaramar Hukumar Tarauni, Hajiya Halima.

A ƙarshen gasar, an bayyana Abdullahi Dauda na Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Walawai a matsayin wanda ya zo na farko, yayin da Hafsat Malam Liman ta Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Maituw o ta zo ta biyu.

Isma’ila Sulaiman na Darmanawa ya zo na uku, yayin da Usman Sani na Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Unguwar Gano ya zo na huɗu.

An ba waɗanda suka yi nasara kyaututtuka daban-daban domin ƙarfafa musu gwiwa.

By ukarofi

Leave a Reply