Shugaban Paraguay ta bada hutu bayan ƙasar ta doke Jamus a gasar Kofin Duniya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Santiago Pena na Paraguay ya ayyana ranar Talata, 30 ga Yuni a matsayin hutu ga ‘yan ƙasarsa bayan da ta doke Jamus a zagayen ‘yan 32 a wasan gasar Kofin Duniya da ke gudana a Nahiyar Amurka.

Paraguay ta samu nasarar hayewa zuwa zagaye na gaba ne bayan nasara da 4 da 3 a bugun fenarati bayan Kai Havertz ya farke ƙwallon da Julio Enciso ya zura wa Jamus.

Wannan sakamako ya sa a karon farko a tarihi ‘yan wasa maza na Jamus sun rasa nasara a zangon bugun fenarati a gasar Kofin Duniya.

By Babaji

Leave a Reply