Sin na shan yabo kan gudunmawarta ga kare muhallin duniya

Daga AHMAD FAGAM

Muhalli shi ne rayuwa, dukkan halittu na buƙatar kyautatuwar muhalli domin samun rayuwa mai inganci da walwala. A yayin da aka gudanar da bikin ranar muhalli ta ƙasa da ƙasa a ƙarshen wannan mako, masu ruwa da tsaki suna ci gaba da jaddada muhimmancin kare muhalli da yin kiraye-kirayen a kaucewa gurɓata muhallin halittu, domin samun rayuwa mai inganci gami da kaucewa shiga mawuyacin hali a sakamakon gurɓacewar muhallin.

A jawabin da ya gabatar a jajiberin bikin muhalli na shekarar 2022, babban sakataren MƊD Antonio Guterres, ya ce ana buƙatar abubuwa masu tarin yawa a wannan duniyar tamu domin tafiyar da rayuwarmu yadda ya kamata, kuma abubuwan dake lalata muhalli ba kawai suna cutar da duniya ba ne, har ma da halittun dake rayuwa cikinta. An yi ƙiyasin sama da mutane biliyan 3 ne matsalolin taɓarɓarewar muhallin halittu ya shafa a duniya.

Kana gurɓacewar muhalli yana sanadiyyar mutuwar wuri na kusan mutane miliyan 9 a duk shekara a duniya, sannan sama da nau’ikan dabbobi da tsarrai miliyan 1 ne ke fuskantar barazanar bacewa daga doron ƙasa a duk shekara a duniya, kamar yadda babban jami’in MƊDr ya bayyana. Ya ce nan da shekarar 2050, sama da mutane miliyan 200 ne a duk shekara za su fuskanci barazanar barin muhallansu sakamakon matsalolin sauyin yanayi.

Bisa lura da girman matsalolin da duniya ke fuskanta, ya sa mahukuntan ƙasar Sin ke tsayawa tsayin daka, wajen sauke nauyin dake bisa wuyansu na kare muhalli a mataki na cikin gida har ma da matakin ƙasa da ƙasa.

Matakan da ƙasar Sin ke ɗauka wajen kare muhalli ya yi matukar ɗaukar hankalin ƙasa da ƙasa, kamar yadda Elizabeth Maruma Mrema, babbar sakatariyar sashen kula da nau’ikan halittu ta MƊD ta ce, ƙasar Sin ta cimma muhimman sakamako masu ƙarfafa gwiwa a fannonin yaki da matsalar sauyin yanayi, da kandagarkin bacewar nau’in halittu, da rage iska mai gurbata muhalli.

Mrema ta yi wannan tsokaci ne a lokacin bikin ranar kare muhalli ta ƙasar Sin ta shekarar 2022, inda ta bayyana hakan a jawabin da ta gabatar. Taken bikin na bana shi ne, “mu yi aiki tare don gina kyakkyawar duniya mai tsafta.”

Jami’ar MƊD ta ce, ƙasar Sin ta yi aiki tukuru, tare da bayar da gagarumar gudunmawa ga ƙoƙarin da duniya ke yi wajen magance matsalolin dake shafar muhalli, da daga matsayin aikin gina cigaba mai dorewa, da kuma gina makomar al’umma don kyautata rayuwar dukkan bil adama a duniya.

Bugu da ƙari, ta kuma yabawa matakan da kasar Sin ke ɗauka wajen kiyaye nau’ikan halittu, matakan da suka haɗa da kafa lambunan shan iska na ƙasa, da kuma samar da dokokin dake shafar kiyaye muhallin halittu. Guterres ya buƙaci gwamnatoci da su bada fifiko wajen ɗaukar matakan tinkarar matsalolin sauyin yanayi, da kare muhalli, ta hanyar ɓullo da manufofin da zasu taimaka wajen tabbatar da ci gaba mai ɗorewa.

Cikin wasiƙar da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya aike don taya murna bikin ranar muhalli ta ƙasar Sin na shekarar 2022, ya yi nuni da cewa, muhallin halittu shi ne ginshikin rayuwa da ci gaban dan Adam, kuma kiyaye muhalli yadda ya kamata shi ne burin bai ɗaya na jama’ar ƙasashe daban daban. Ya ce tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta ƙasar Sin karo na 18, ƙasar Sin ta dauki aikin raya al’adun halittu a matsayin wani muhimmin shiri mai alaƙa da samun dauwamammen ci gaban al’ummar ƙasar, tana kuma tsayawa kan ra’ayinta na “tabbatar da kyakkyawan muhalli shi ne arzikinmu”.

Ranar muhalli ta duniya, ta kasance a matsayin wani muhimmin lokaci da MƊD ke amfani da shi, wajen faɗakar da duniya game da matakan da suka dace a ɗauka don kare muhalli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *