‘Yan sanda sun tsaurara tsaro ga Salman Khan don kare shi daga barazanar kisa

Daga AISHA ASAS

Biyo bayan tsananta bincike kan kisan da aka yiwa mawaqi Sidhu Moose Wala, jami’an tsaro sun bankaɗo Lawrence Bishnoi a matsayin wanda ake zargin da sa hannunsa a kisan, wanda ya kasance barazana ga babban jarumi Salman Khan.

Da yake jawabi ga jaridar Hindustan Times, babban ɗan sanda na rundunar ‘yan sanda ta Mumbai ya ce, “mun ƙara tsaurara tsaro ga Salman Khan cikin ‘yan kwanakin nan, mun sanya jami’an tsaro sun kewaye gidansa, kowanne lungu da saƙo mun saka ido don tabbar da duk wani shiri na ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Rajasthan kan jarumin bai kai ga nasara ba.”

Bishnoi ya tava bayyana ƙudurinsa na aika jarumin lahira don ɗaukar fansa kan saka kansa da ya yi a farautar ƙungiyar blackbuck wadda shi Bishnoi ke ciki.

A shekara ta 2008, a wajen kotu, Lawrence Bishnoi ya yi iƙirarin kashe Salman Khan a bainar jama’a. ya kuma ƙara da cewa, “idan muka tashi ɗaukar mataki kowa ma zai sani. Ba dai yanzu an tuhume ni da laifukan da ban aikata ba.”

A shekara ta 2020 ne aka kama abokin harƙallar Bishnoi, wato Rahul Alias, kan zargin kisan kai, inda ya bayyana cewa, tuni sun ƙyanƙyashe shirin farautar rayuwar jarumi Salman Khan. Kuma rundunar ‘yan sandar Mumbai sun samu labarin shigowar Bishnoi ƙasar, wanda suke zargin ya zo cika alƙawarin da ya ɗauka kan jarumin.