Manoman Jihar Xinjiang suna girbin hatsi

Daga CMG HAUSA

A halin da ake ciki yanzu, manoman jihar Xinjiang na ƙasar Sin suna girbin alkaman da aka shuka a yanayin sanyi, kuma an yi hasashen cewa, farashin hatsin da adadin hatsin da za a saya za su karu sannu a hankali.

Rahotannin da hukumar adana hatsi da kayayyaki ta jihar Xinjiang mai cin gashin kanta ta fitar sun nuna cewa, sassa daban daban na jihar suna gudanar da ayyukan tattara kudi, da keɓe wuraren adana hatsi, da kashe ƙwayoyin cuta a wuraren, da tantance na’urorin da za a yi amfani da su, da kuma horas da ma’aikatan da abin ya shafa, domin tabbatar da cewa, manoman za su sayar da hatsin lami lafiya.

Gaba daya adadin alkamar da za a sayar a jihar zai kai tan miliyan 3.5, kuma farashin alkamar kan kowane kilo zai kai kuɗin Sin yuan 2.68, adadin da zai karu da yuan 0.15 a bisa makamancin lokacin bara, kana kamfanoni 450 ne za su shiga aikin sayen hatsin.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa