Zaɓen fidda gwani a APC: Buhari da gwamnonin Arewa sun shiga ganawar sirri a kan tikitin takarar shugaban ƙasa

Daga AMINA YUSUF ALI

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi taron ganawar sirri tare da dukkan gwamnonin Arewa na APC a fadarsa ta shugaban ƙasa dake Abuja.

Taron ya zo ne sa’o’i kaɗan kafin zaven fidda gwani na ɗan takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC wanda ya wakana a ranar Litinin a Eagle Square dake Abuja.

Kodayake, ba a samu wani sahihin bayani game da dalilin da ya sa aka yi ganawar ba, amma ana ganin ganawar ba ta rasa nasaba da samun nasara a wajen zaɓen fidda gwanin da za a gudanar ba.

Wannan dai shi ne karo na huɗu da aka yi taron ganawa a tsakanin shugaban Buhari da masu ruwa da tsaki a jam’iyyar a game da zaɓen fidda gwani na cikin jam’iyyar APC.

Bayan ganawarsa da gwamnonin APC a ranar Talatar makon da ya gabata, Buhari ya yi taron ganawa da dukkan masu neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar. Inda ya nemi da su tattauna da juna don fidda ɗan takara ma fi dacewa daga tsakaninsu.

Mahalarta taron sun haɗa da, shugaban ƙungiyar gwamnonin APC, Atiku Bagudu (Kebbi); Shugaban gwamnonin Arewa, Simon Lalong; Abubakar Bagudu (Jigawa) da Babagana Zulum (Borno).

Sauran sun haɗa da Aminu Bello Masari (Katsina); Abdullahi Sule (Nasarawa); Bello Matawale (Zamfara); Mallam Nasir El-Rufai (Kaduna); Abdullahi Ganduje (Kano); Yahaya Inuwa (Gombe); Abubakar Bello (Neja) da kuma Mai Mala Buni (Yobe).