Yadda take kulawa da buƙatun ƙasashe masu tasowa ya sa ƙasar Sin ta zama aminiyarsu

Daga BELLO WANG

A kwanan baya, ministan harkokin wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya ziyarci wasu ƙasashe tsibirai dake yankin tekun Pasific, daga bisani ya bayyana cewa, “ Kar a bar ƙasashe marasa ƙarfi su ci gaba da fama da matsalar koma bayan tattalin arziki.” Maganarsa ta nuna buƙatar ƙasashe masu tasowa ta neman samun ci gaba da wadata, da kuma dalilan da suka sanya ƙasar Sin ke samun goyon baya daga ƙasashen masu tasowa, wato saboda yadda take kulawa da bukatunsu.

Wani bayani da wata ƙwararriyar a fannin tattalin arziki ta kasar Kenya Anzetse Were ta rubuta, wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na mujallar Diplomat ta ƙasar Amurka a kwanan baya, shi ma ya tabbatar da gaskiyar ra’ayina. Wannan bayani mai taken “Sirrin ƙasar Sin game da manufarta da ta shafi tattalin arzikin ƙasashen Afirka” ya nuna dalilin da ya sa ƙasashen Afirka suke nuna goyon baya ga ƙasar Sin.

Da farko dai, a cewar Madam Anzetse, ƙasar Sin tana nuna daidaito ga kasashen Afirka.

Saboda yadda take bin manufofi na “zama daidai wa daida”, da “rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran ƙasashe”, ƙasar Sin ba ta taba neman yin shisshigi a nahiyar Afirka ba, ko kuma tilastawa ƙasashen Afirka bin tsarinta. Yayin da a nasu ɓangaren, ƙasashen yamma suna tsammanin cewa, ya kamata ƙasashen Afirka su bi dukkan shawarwarinsu, ko da yake, sun taba yi wa nahiyar mulkin mallaka.

Na biyu shi ne, domin ƙasar Sin tana girmama ‘yancin ƙasashen Afirka na yin zabi bisa ra’ayin kansu.

Bayan da ƙasashen Afirka sun yi kira da a ba su karin damammaki na yin ciniki maimakon ba da tallafi kawai, ƙasar Sin ta amshi kiran a farko. Daga bisani, ƙasar Sin da kasashen Afirka sun fi mai da hankali kan haɗin gwiwar tattalin arziki, da raya ɓangaren kayayyakin more rayuwa, da sauran batutuwan da suka fi janyo hankalin ƙasashen Afirka. Yayin da a nasu ɓangaren, ƙasashen yamma suke kallon kansu a matsayin abin koyi ga ƙasashen Afirka, ko da yake tsarinsu na raya tattalin arziki na fuskantar dimbin matsaloli, da suka haɗa da rashin daidaituwa tsakanin al’umma, da yawan samun tashin hankali, da masu fama da talauci, da dai sauransu.

Na uku, shi ne ƙasar Sin ta fahimci yanayin da ƙasashen Afirka ke ciki.
Saboda ƙasar Sin ta taba kasancewa a yanayi iri daya da ƙasashen Afirka, a fannin ci gaban tattalin arziki, don haka ta fahimci bukatun ƙasashen Afirka sosai. Wannan dalili ya sa haɗin gwiwarta da kasahsen Afirka ke samar da dimbin alfanu ga ƙasashen. Misali, aikin gina kayayyakin more rayuwa a Afirka da ƙasar Sin ta zuba jari a ciki yana taimakawa rage gibin da ake samu tsakanin yankunan Afirka a fannin tattalin arziki, da rage tsawon lokacin da ake warewa da makamashin da ake konawa wajen yin zirga-zirga, da samar da ɗimbin guraben aikin yi, da damammaki na ciniki, da miƙa sabbin fasahohi da ilimi masu alaka da wannan fanni ga bangaren Afirka.

Yayin da a nasu ɓangaren, ƙasashen yamma suke ci gaba da tsammanin cewa, ana yabawa kan yadda suke samun ci gaban tattalin arziki, kana ƙasashe daban daban na son ganin wata babbar ƙasa daga yammacin duniya ta zama mai fada a ji a duniya, domin hakan zai tabbatar da makomar duniya mai haske.

Amma a sabanin haka, yadda ƙasashe masu tasowa suke nuna rashin gamsuwa da tsarin kula da harkokin duniya ƙarƙashin jagorancin ƙasashen yamma, shi ma ya kasance daya daga cikin manyan dalilai da suka sa ƙasashen Afirka ke nuna ƙarin goyon baya ga ƙasar Sin, wata babbar ƙasa da ta sha bamban da ƙasashen yamma.