Sojoji sun cafke mai kitsa hare-haren boma-bomai da wasu a Borno

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun rundunar sojoji ƙarƙashin jagorancin atisayen Haɗin Kai (OPHK), sun yi nasarar kama Shariff Umar da ake kira da Yusuf, wanda ake ganin shi ne mai alhakin shirya hare-haren tayar da boma-bomai da ƙulla makirce-makirce a Borno da wasu jihohin Arewa ta Gabas.

Jami’in yaɗa labaran jami’an haɗaka na atisayen a yankin, Laftanal Kanal Sani Uba ne ya sanar da haka a wata takarda ranar Asabar a Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno.

A cewarsa, bincike ya nuna cewa Umar na taka muhimmiyar rawa wajen ɗauka, bada horo da aika ‘yan ƙunar baƙin-wake. Haka kuma ya kan sanya ido akan kayan aikin ‘yan ta’adda da isar da kayan haɗa boma-bomai.

Sannan, a binciken an gano cewa mutumin shi ne wanda ya shirya harin ƙunar baƙin-wake na ranar 24 ga watan Disamba, 2025, da wani mai suna Adamu ya kwance wata rigar bom a Masallacin Kasuwar Gamboru, lamarin da ya yi sanadin mutuwar masallata da jikkata wasu da dama.

Sannan, ya kitsa wani daƙilallen hari a Damaturun jihar Yobe, inda ya damƙa wa ɗan ƙunar baƙin-wake ababen fashewa gabanin daƙile harin.

Binciken sun ƙara bayyana cewa, matarsa, Yagana Modu tana hannu a aikata miyagun laifukan yayin da agolar gidansa kuma, wato Amina, an ruwaito cewa ta ga wani da ake zargi yana ɗauke da bom a gidansu.

Wannan nasara ta taimaka wajen gano yadda masu taimaka wa ‘yan ta’adda ke amfani da dabaru a gidaje da unguwanninsu domin aiwatar da ayyukansu.

A yanzu haka dai an kama mutane 14 ciki har da Umar, waɗanda ake gudanar da bincike mai zurfi akansu domin katse baki-ɗaya hanyoyin da suke bi wajen tada zaune-tsaye a shiyyar, gano sauran masu aiki tare da su da kuma ƙoƙarin gano sauran ababen fashewar.

A ƙarshe, Kakakin na OPHK bayyana cewa haɗin kan jama’a da bayanai na sirri sun taimaka wajen kai su ga samun nasarar, yana mai kira gare su da cigaba da kasancewa a ankare game da al’amuran da ke faruwa a yankunansu tare da ruwaito dukkan wani abin zargi.

By ukarofi