SPRING ta shirya taron ƙara wa juna sani kan yaƙi da cin zarafin mata da yara

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wata cibiyar ƙarfafa zaman lafiya da samar da mafita kan cin zarafin mata (SPRING) da ƙasar UK ke ɗaukar nauyi,ta shirya taron ƙarawa juna sani mai taken ‘mata ,zaman lafiya, tsaro da yaƙi da cin zarafin mata ‘a Katsina.

Wannan shiri na SPRING da UK ta ɗsuki nauyi ,shiri ne na tsawon shekaru huɗu da ke gudana a Arewacin ƙasar.

A wata hira da manema labarai,manajan shirin na wannan yankin Alhaji Abdulkadir Sambo ya ce an shirya taron ƙarawa juna sani domin ƙarfafa kuzari na masu ruwa da tsaki kan wannan yaƙi da cin zarafin mata da kyautata zamantakewa a tsakanin al’umma.

Ya bayyana rikice rikicen a mafi yawan lokutan da ya ke faruwa,mata da ƙananan yara ke shafa.

” Ba wai muna duba abinda ya shafi mata da yara ba kawai har da tunanin al’ummqa kan yadda rikicin ya fi shafar su”Inji Sambo.

Sambo ya bayyana cewar a nan jihar Katsina sun yi tsare-tsaren a shekarar baya ba yadda “zamu haɗa kai domin cigaba da aiwatar da tsare-tsare da za a samu ɗorewar zaman lafiya”.

By ukarofi