Tallafa wa ta’addanci: CBN ya ƙara tsaurara bincike kan bankuna

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara tsaurara sa ido da bincike kan bankuna da sauran cibiyoyin kuɗin ƙasar, musamman wajen gano haɗarin amfani da tsarin kuɗin ƙasar wajen tallafa wa ayyukan ta’addanci.

Matakin na daga cikin ƙoƙarin hana masu aikata laifuka amfani da tsarin hada-hadar kuɗi na Nijeriya wajen ɓoye ko jigilar kuɗaɗen da ake amfani da su wajen ayyukan ta’addanci.

CBN ya ce, ya ɗaga batun sa-ido kan hanyoyin samar da kuɗin ta’addanci zuwa cikin muhimman abubuwan da yake bai wa fifiko a halin yanzu. Hakan ya sa aka ƙara mayar da hankali kan bibiyar hada-hadar kuɗi, bayar da rahoton ma’amalolin da ake zargi, da kuma aiwatar da takunkuman kuɗi na musamman da aka ƙaƙaba wa wasu mutane ko ƙungiyoyi.

Babban bankin ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Muƙaddashiyar Daraktar Sashen Sadarwa da Hulɗa da Masu Zuba Jari, Hakama Sidi-Ali, ta sanya wa hannu ranar Talata.

CBN ya ce, ƙara tsaurara sa-ido kan harkokin samar da kuɗin ta’addanci na daga cikin ci gaba da matakan da yake ɗauka domin kare tsarin hada-hadar kuɗi na Nijeriya daga amfani da shi wajen ayyukan haramtattu.

Matakin na nufin bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi da hukumomin gwamnati ke sa ido a kansu za su fuskanci ƙarin bincike kan tsarin da suke amfani da shi wajen gano tare da kula da hada-hadar kuɗin da ka iya kasancewa da alaƙa da tallafa wa ta’addanci.

A cewar CBN, sa-idon zai fi mayar da hankali kan muhimman fannoni guda huɗu: kula da haɗarin samar da kuɗin ta’addanci, bibiyar hada-hadar kuɗi, aiwatar da takunkuman kuɗi na musamman, da kuma bayar da rahoton ma’amalolin da ake zargin suna da alaƙa da tallafa wa ta’addanci.

Saboda haka, ana sa ran bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi da ake sa wa ido za su tabbatar da cewa suna da ingantattun tsare-tsare da za su iya gano hada-hadar kuɗi da ba ta saba da tsarin abokan cinikinsu ba, tare da bin ƙa’idojin yaƙi da halatta kuɗaɗen haram da kuma yaƙi da samar da kuɗin ta’addanci.

CBN ya kuma ce zai ci gaba da amfani da tsarin sa-ido bisa la’akari da irin haɗarin da wata cibiya ko harkar kuɗi ke iya haifarwa. Wannan ya haɗa da gudanar da bincike kai tsaye a cibiyoyin kuɗi da kuma sa-ido daga nesa ba tare da zuwa wurinsu ba.

Babban bankin ya ce tsarin zai taimaka wajen tabbatar da cewa matakan yaƙi da halatta kuɗaɗen haram, samar da kuɗin ta’addanci da kuma samar da kuɗaɗen da za su iya taimaka wa yaɗuwar makaman kare dangi suna aiki yadda ya kamata, bisa dokoki da ƙa’idojin da ake da su.

Tsarin sa-ido bisa la’akari da haɗari na nufin ba a bai wa dukkan bankuna, abokan ciniki ko ma’amaloli matakin bincike iri ɗaya ba. Maimakon haka, ana fi karkata hankali ne kan cibiyoyi, mutane, hada-hadar kuɗi ko ayyukan da ake ganin suna da babban haɗarin aikata laifukan kuɗi.

Sabon matakin ya kuma ƙara jaddada muhimmancin aiwatar da takunkuman kuɗi na musamman. Waɗannan takunkumai na da nufin hana mutanen da aka ayyana ko ƙungiyoyin da aka sanya wa takunkumi samun damar amfani da tsarin hada-hadar kuɗi wajen karɓa ko tura kuɗi.

Haka kuma, bayar da rahoton ma’amalolin da ake zargi na daga cikin abubuwan da CBN ya fi mayar da hankali a kai. A ƙarƙashin ƙa’idojin da ake da su, ana buƙatar cibiyoyin kuɗi su rika bibiyar harkokin abokan cinikinsu tare da kai rahoton duk wata ma’amala da ta haifar da zargin aikata laifukan kuɗi.

CBN ya ce ƙara tsaurara sa-idon na daga cikin manyan matakan da Nijeriya ke ɗauka a cikin gida da kuma haɗin gwiwa da ƙasashen duniya wajen daƙile samar da kuɗin ta’addanci da sauran barazanar da ka iya lalata amincin tsarin hada-hadar kuɗi.

Babban bankin ya ƙara da cewa zai ɗauki wasu matakan sa-ido ko gudanar da bincike idan buƙatar hakan ta taso.

Wannan sabon matakin ya biyo bayan umarnin CBN na ranar 24 ga Yunin 2026, inda ya umurci bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi da su gaggauta daskarar da asusun ajiyar kuɗi da kadarorin wasu mutane da kamfanoni da aka sanya wa takunkumi saboda ta’addanci ko tallafa wa ta’addanci.

Umarnin yana cikin wata sanarwa da Sashen Kula da Bin ƙa’idoji na CBN ya fitar, wadda aka aika wa bankuna, Bankunan Ayyukan Biyan Kuɗi da sauran cibiyoyin kuɗi da ke ƙarƙashin dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi ta 2020.

A cewar sanarwar, matakin ya biyo bayan ayyana wasu mutane da ƙungiyoyi a matsayin waɗanda aka sanya wa takunkumi daga hannun Kwamitin Takunkuman Nijeriya da kuma Ofishin Kula da Kadarorin ƙasashen Waje na Ma’aikatar Baitulmali ta Amurka, ƙarƙashin Dokar Zartarwa mai lamba 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima, kan batutuwan ta’addanci da samar da kuɗin ta’addanci.

By ukarofi

Leave a Reply