
Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Talata ne Fadar Shugaban Ƙasa ta ce aƙalla manyan motoci 200 na man fetur ne za a riƙa samarwa a kowacce rana daga matatar mai ta Fatakwal dake Jihar Ribas.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X, Mai taimaka wa shugaban ƙasa na musamman kan harkar Sadarwa da Wayar da kan al’umma, Sunday Dare ya ce matatar ta sake dawowa don cigaba da aiki, wadda ake sa ran za ta riƙa samar da ganga 60,000 a kullum.
Da farko dai Kamfanin Man Fetur na Ƙasa, NNPCL ya sanar da cewa matatar ta koma aikin tace ɗanyen mai bayan alƙawuran da aka sha yi a baya na dawowarta aiki.
A shekarar 2021 ne Gwamnatin Tarayya ta ware Dala biliyan 1.5 don gyaran matatar, wadda ta na ɗaya daga cikin manyan matatun Nijeriya, shekaru biyu bayan rufe ta.
Duk da cewa Nijeriya ta na ɗaya daga cikin ƙasashe masu yawan albarkatun mai, amma ta dogara ne da man da ake shigowa da shi daga wasu ƙasashe sakamakon rashin wajen tacewa.
