Tarihin Sarkin Dutse, marigayi Mai Martaba Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Marigari Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Nuhu Muhammad Sanusi, CFR. Mutum ne mai ilimin addini da na zamani, ɗankasuwa, kuma mai son kyautatawa jama’arsa.

Yana da jajircewa wajen ganin an aikata gaskiya a dukkan hali. Mutum ne mai son tafiye-tafiye. Rubutun da mai karatu zai karanta dangane da rayuwar Mai Martaba Sarki Nuhu Muhammadu Sanusi, an tsakuro shi ne daga littafin da shi Mai Martaba Sarki ya rubuta da hannunsa mai suna ‘The Days in My Life’.

An haife ni da safiyar ranar Juma’a 5 ga watan Janairu na shekarar 1945 wanda ya yi daidai da 20 ga watan Muharram na shekarar hijira ta 1364, a garin ‘Yar Gaba. Daga wannan gari na ’Yar Gaba, ana iya hango duwatsun garin Dutse fadar masarautar Dutse. Sunan mahaifiyarsa Fatsumatu wacce ta ke ita ce babbar matar mahaifin mai martaba sarki.

Karatu:

Mai Martaba Sarki Nuhu Muhammad Sanusi ya ce, “An saka ni a makarantar Ƙur’ani a lokacin da nake da shekarau 4, a cikin wannan ƙauyen.

Na fara da koyon harrufan Larabci cikin yaren Fullanci kafin daga baya na koma harshen Hausa.

Bayan na gama na koma furuci sannan kuma na kama Haddar gajerun surorin Al-ƙur’ani mai girma, a qarshe kuma na koyi rubuta Al-ƙur’ani a kan allo”.

Ya ci gaba da cewa, “An saka ni a makarantar elemantare a ranar 1 ga watan Afrilu na shekarar 1952 aka saka ni a ajin share fagen shiga firamare (pre-primary class) tare da wasu yara maza 16 da mata 7 sa’annina da aka zazzaɓo daga wasu ƙauyukan na yankin Dutse”

Mai martaba sarki ya gama wannan makaranta a shekarar 1956, daga nan kuma sai babbar firamare (senior primary school) da ke Birnin Kudu, daga 1957 zuwa 1959.

Bayan kammala karatunsa kuma a wannan makaranta sai ya wuce zuwa ƙaramar makarantar sikandire inda ya samu zuwa Gwarzo a shekarar 1960 zuwa 1961.

Ya kammala karatunsa na kwalejin horas da malamai (teachers college) daga 1961 zuwa 1966 a garin Kano. Daga nan kuma sai Babbar kwalejin horas da malamai (Advance Teachers College) da ke Kano daga 1967 zuwa 1970.

Bayan kammala wannan makaranta mai martaba sarki ya samu nasarar zuwa Jami’ar Ohi da ke ƙasar Amurka inda ya samu digiri a fannin Kuɗi (Degree in Finance) daga shekarar 1971 zuwa 1974. Ya kuma yi karatu a jami’ar ‘Brandford’ da ke ƙasar Ingila a shekarar 1977.

Gogayyar aiki:

Bayan Kammala karatunsa da ya yi, mai martaba sarki ya yi ayyuka tare da gurare da dama, daga ciki akwai: ya koyar a makarantar “Kano Staff Development Centre”, sai kuma Jami’ar Bayero a matsayin babban laccara (senior lecturer), sai kuma hukumar ALDA a matsayin jami’in kasuwanci (marketing manager), sai kuma ‘New Nigerian Development Company (NNDC)’, 1976.

Daga nan kuma sai ‘Mambilla-Coffee and Tea Plantation’, 1976 zuwa 1979. Ya zama mamba na hukumar jiragen sama ta Nijeriya (Board member Nigerian Airways) a shekarar 1984 zuwa 1985, zamanin mulkin soja na shugaba Muhammadu Buhari. Ya kuma yi aiki da kamfanin Isyaku Rabi’u (Isyaku Rabi’u Group of Companies). Tun daga shekarar 1986 zuwa 1995 sai ya koma mai cin gashin kansa. Sannan ya halarci taron yin dokoki (constitutional conference) daga 1988 zuwa 1989.

Zamowarsa sarki:

Tun kafin zamowarsa sarkin Dutse, mai martaba sarki ya riqe muƙamin Babban ɗan majalisar sarki, muƙamin da gwamna Ali Sa’adu Birninkudu ya yi masa a shekarar 1992, wanda aka tabbatar da shi a ranar 17 ga watan Mayu na shekarar 1992.

Bayan rasuwar mahaifinsa a ranar Larabar 29 ga watan Nuwamba na shekarar 1995, gwamnan jahar Jigawa na wannan lokacin, Kanal Ibrahim Aliyu ya tabbatar da shi a matsayin sabon sarkin Dutse.

Mutuwa:

Allah ya yi wa Sarkin Dutse, Nuhu Muhammad Sunusi rasuwa ranar 31 Ga watan Junairu 2023 yana da shekaru 79 a duniya

Sarkin ya rasu ne a Abuja bayan ya yi fama da jinya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *