Tattalin arziki Nijeriya ya gama tsaya wa da ƙafarsa — Shettima

Spread the love

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya tabbatar wa masu zuba jari cewa yanzu ne lokacin da ya fi dacewa su zuba jari a Nijeriya, domin ƙasar ta fice daga halin rashin daidaiton tattalin arziki.

Ya bayyana haka ne a wajen babban taron zuba jari na ‘Bauchi Investment Summit 2025’ a Jihar Bauchi, inda ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kawar da manyan cikas da suka hana ci-gaban tattalin arziƙin ƙasa.

Ya bayyana cewa, a yanzu kudaden da ake kashewa wajen biyan bashi sun sauka zuwa ƙasa da kashi 50 cikin ɗari daga sama da kashi 100, yayin da tattalin arzikin ƙasar (GDP) ya karu zuwa kashi 4.23 cikin ɗari.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ƙara da cewa an samu ƙaruwa mai yawa a fannin haraji da kuɗaɗen shiga da ba na mai ba, wanda ya tashi da kashi 411 cikin ɗari cikin shekara guda. Ya ƙara da cewa ajiyar kudin ƙasar a ƙasashen waje ya kai dala biliyan 43 a watan Satumba 2025, yana mai cewa, “Najeriya ta fita daga halin rashin tabbas, don haka yanzu ne lokacin da ya fi dacewa masu zuba jari su zabi Najeriya.”

Kazalika, ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakan cire tallafin mai da daidaita tsarin musayar kuɗi domin samar da dawwamammen ci gaba da kwanciyar hankali a harkokin tattalin arziki.

Da yake jawabi, Gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed, ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bisa halartar taron tare da tabbatar da cewa gwamnati za ta aiwatar da shawarwarin da aka cimma a taron.

Haka kuma, Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad III, ya yi kira ga gwamnoni da shugabanni na Arewa da su mayar da hankali wajen aiwatar da sakamakon irin waɗannan taruka, yana mai cewa Arewa na da isassun albarkatu da za su iya fitar da yankin daga matsalolin tattalin arziki idan aka yi amfani da su yadda ya kamata.

By Babaji