
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin Dakta Olugbemisola Titilayo Odusote a matsayin darakta-janar ta Makarantar Horar da Lauyoyi ta ƙasa. Naɗin nata zai fara aiki ne daga ranar 10 ga watan Junairu, 2026, inda za ta shafe tsawon shekaru huɗu a muƙamin.
Dakta Titilayo Odusote mai shekaru 57, ita ce mataimakiyar shugaban makarantar, wadda kuma za ta maye gurbin Farfesa Isa Hayatu Chiroma da zai kammala wa’adinsa a ranar 9 ga Janairu.
Haka kuma, ita ce mace ta farko da za ta jagoranci makarantar tun bayan buɗe ta a shekarar 1962.
Ta kammala digirinta na farko a fannin shari’a (LL.B.) da zama lauya a shekarar 1988 a Jami’ar Obafemi Awolowo. Sannan ta ta yi digiri na biyu a fannin hallau, wato LL.M a jami’ar, inda ta samu ƙwarewa a shari’ar kamfani da kasuwanci.
Daga bisani ta garzaya Jami’ar Surrey da ke Birtaniya inda ta yi na uku (PHD), a fannin binciken shari’ar al’umma da gudanarwar adalci.
Ta fara aiki a makarantar lauyoyin ne a matsayin lakcara a shekarar 2001. Tun lokacin, ta riƙe muƙamai daban-daban ciki hat da shugabar sashen karatu, daraktar kararu da kuma shugabar makaranta.
Kazalik, a yayin aikinta na makarantar, ta kan je koyarwa a Jami’ar Nottingham Trent da ke Birtaniya na gajeren zango.
