Tinubu ya soke naɗin Ɗakingari a matsayin jakadan Turkiyya sa’o’i bayan sanarwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya soke naɗin tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, Usman Isa Ɗakingari Suleiman a matsayin jakadan Nijeriya a Turkiyya sa’o’i kaɗan bayan Fadar Shugaban Ƙasa ta sanar da tura shi ƙasar.

A wata sanarwa da Kakakin Shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya fitar da fari, Shugaba Tinubu ya amince da tura jakadu guda huɗu daga jaddawalin 68 da Majalisa Dattawa ta tabbatar a Disamba.

Sanarwar ta ce, shugaban ƙasar ya amince da tura Ambasada Ayodele Oke a matsayin jakadan Nijeriya zuwa ƙasar Faransa, yayin da Kanal Lateef Are zai wakilci Nijeriya a Amurka.

Haka kuma, an amince da tura Ambasada Aminu Ɗalhatu, wanda tsohon jakadan Nijeriya ne a ƙasar Koriya ta Kudu, a matsayin Babban Kwamishina zuwa Birtaniya.

Sai na huɗunsu, wato Sa’idu Usman Ɗakingari, tsohon Gwamnan Jihar Kebbi, a matsayin wanda zai wakilci Nijeriya a Turkiyya.

Saidai, a sanarwa ta biyu, fadar shugaban ƙasar ta sanar da soke jakadan na Turkiyya tare da tabbatar da waɗancan sauran ukun.

Kazalika, fadar ba ta yi bayanin musabbabin sauyin na kwatsam ba ko kuma sanar da dakatar da jakadancin na Turkiyya na wucin-gadi ko dindindin ba.

Sannan, ba a samu wani bayani da ya ƙunshi makomar Ɗakingari ba a yayin haɗa wannan rahoto.

By Babaji