Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Muhammad Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ne zabinsu a babban zabe na 2027.
Sheikh Jingir, wanda shi ne Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Ikamatis Sunnah (JIBWIS) ya bayyana zabin Tinubu ne a yayin taron kara wa juna sani na shekarar 2026 da kungiyar ta shirya a garin Jos.
Ya ce kungiyar ta yanke shawarar goyon bayan Tinubu idan bai ci amanar ’yan Nijeriya ba. A cewarsa, sun riga sun yi masa alkawarin goyon baya domin ya yi wa’adi na biyu, kuma ba za su saba alkawarin ba.
“Mu ba masu karya alƙawari ba ne. A zaben da ya gabata mun zabe Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu. Mun zabe ka ne domin ka inganta rayuwar mutanen Nijeriya .
“Kada ka ba mu kunya, idan ka yi kuma, mu Allah Ne karfinmu. Za mu goya maka baya ka sake tsayawa takara. Mun yi alkawarin sake zaben ka tare da Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima a 2027,” inji shehin malamin.
Ya bayyana imanin cewa Tinubu ba zai ci amana ba, kuma shi da mataimakinsa suna da kyakkyawar alaka, sabanin jita-jitar zaman doya da manja tsakaninsu da ake yadawa.
“Kun taɓa jin inda Shugaba Tinubu ya zagi Shettima ko ya ci mutuncinsa? Shugaban ƙasa yana ƙaunar mataimakinsa. Kun taɓa ji ko sau ɗaya Shettima ya soki Shugbaba Tinubu? Masu son ganin su a rana kun ji kunya, saboda ba mu taɓa ganin suna faɗa ba, kuma za su gama wa’adinsu na biyu lafiya.
“Mun yi imani cewa Tinubu na kaunar Shettima, kuma da ƙarfin Ikon Allah za su sake cin zaɓe. Zan sake zaɓen su, amma bisa sharaɗin idan sun cika alƙawari.” a cewa Sheikh Jingir.
Ya shawarci Tinubu da ya yi adalci ga kowane dan Nijeriya ba tare da la’akari da addini ko kabila ba, yana mai jaddada cewa Musulunci ba addini ne da aka gina shi bisa turbar kabilanci ba.
