Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Amurka Donald Trump ya ja baya daga barazanar ƙaƙaba wa ƙasashen Turai haraji tare da bayyana cewa ba zai yi amfani da ƙarfin soja wajen karɓar Greenland ba, yankin da ke ƙarƙashin ikon Denmark amma ke da ikon cin gashin kai a wasu fannoni.
Wannan mataki ya zo ne bayan ganawarsa da Sakatare Janar na NATO, Mark Rutte, a gefen taron Dandalin Tattalin Arzikin Duniya da aka gudanar a Daɓos, Switzerland.
A cewar Trump, sun cimma wani tsari na haɗin gwiwa kan makomar Greenland da yankin Arctic, wanda ya ce idan aka kammala shi zai zama alheri ga Amurka da kuma dukkan ƙasashen NATO. Sai dai bai faɗi dalla-dalla kan abin da yarjejeniyar ta ƙunsa ba, lamarin da ya bar mutane da dama cikin tambayoyi kan makomar batun.
Trump ya bayyana a shafinsa na Truth Social cewa tattaunawar ta shafi tsaro, albarkatun ƙasa da sauran muhimman batutuwa. Haka kuma, an tattauna kan shirin “Golden Dome”, wato garkuwar kariya daga makamai masu linzami da Amurka ke shirin kafa wa kanta da abokan hulɗa.
A nasa ɓangaren, Mark Rutte ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a aiwatar da hangen nesan Trump na kare Greenland da ɗaukacin yankin Arctic. Amma lokacin da aka tambaye shi ko Denmark za ta ci gaba da riƙe ikon Greenland, Rutte ya ce wannan batu bai taso ba a tattaunawar.
Tsawon makonni, Trump ya riƙa barazanar kwace ikon Greenland, yana kuma yin barazanar ƙaƙaba haraji kashi 10 zuwa 25 ga Denmark da wasu ƙasashen Turai idan ba a cimma yarjejeniya ba. Wannan ya jawo fargaba game da makomar haɗin kan NATO da kuma kasuwancin da darajarsa ta kai tiriliyoyin daloli tsakanin ɓangarorin biyu.
Denmark dai ta sha jaddada cewa Greenland ba ta sayarwa ba, tare da gargaɗin cewa duk wani yunƙurin amfani da ƙarfi zai iya girgiza tushen NATO.
Matakin da Trump ya ɗauka na dakatar da haraji da janye batun ƙarfin soja ya nuna wani sabon salo na diflomasiyya, kodayake har yanzu akwai shakku kan ko wannan janye-war ta dindindin ce ko kuma dakatawa ta wucin gadi.
Abin da ya rage yanzu shi ne ganin ko wannan sabuwar fahimta za ta haifar da yarjejeniya mai ɗorewa, ko kuma siyasar matsin lamba za ta sake dawowa a nan gaba. Ga ƙasashen Turai da masu bibiyar harkokin duniya, wannan mataki na Trump na iya zama wata dama ta sake gina amincewa a huldar ƙetare, musamman a yankin Arctic mai muhimmanci ta fuskar tsaro da albarkatu.
