Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi kira ga jami’an tsaro a jihar kan su yi riƙo da adalci da sa ido da wajen gudanar da ayyukansu yana mai ba su tabbacin cewa gwamnatinsa ba za ta ci dunduniyar gwamnatin tarayya ba musamman kan abin da ya shafi tsaro duk da kasancewarsa a jam’iyyar adawa.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wurin kwamitin tsaro a ranar Litinin wanda aka yi a fadar gwamnatin jihar da ke Bauchi.
“Mun yarda da dunƙulalliyar ƙasa. Mun yarda matsayin gwamnatin tarayya ba tare da la’akari da matsayimu k-o a kasin haka. Ba yadda za mu yi aiki ba ma jituwa,” ya bayyana.
“Shugabanci ya dogaro ne da tsaro. Lallai ne jami’an tsaro su yi aiki da sarakuna da sauran shugabanni domin tabbatar da sahihancin bayanan sirri da samun tasirinsu da kare afkuwar laifuka,” ya faɗa.
Ya kuma jaddada cewa akwai buƙatar haɗa kai tsakanin sakarakuna domin samun zaman lafiya mai ɗorewa da tsaro a jihar, yana mai ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ɗauki matakai wajen kula da tsaro da hana afkuwar tashe-tashen hankula.
“Duk da cewa jihar Bauchi tana cikin zaman lafiya, akwai barazana ta satar mutane da laifuka da ake yi a iyakokin jihar da bayanan ƙarya da laifuka da ake yi a cikin gari da suke buƙatar an ƙara sa ido da ɗaukar mataki a kansu,” inji gwamnan.
A yayin da yake jaddada muhimmancin musayar bayanan sirri a tsakanin jami’an tsaro da shugabannin al’umma, musamman kan abin da ya shafi dazuka da kasuwanni da wurarenda ake da cincirindon al’umma. Ya yi gargaɗin cewa ƙaramin laifi na iya zama babba idan ba a magance matsalar ba.
Gwamnan Bala Mohammed ya yi kira ga sakaruna kan su ba da gudunmowa wajen shiga tsakani da tattara bayanai da jan hankalin al’umma. Sai dai ya ce, akwai buƙatar yin takatsantsan wajen handame filaye domin hakan na iya kawo naƙasu ga matslar tsaro.
“Yin shiru kan aikata laifi na nufin goyon bayan laifi. Sarakuna ba su da bambanci da gwamnati domin muhimmancinsu ga sha’anin mulki,” inji gwamnan.
“Tsaro nauyi ne a kan kowa. Lallai ne mu yi aiki tare domin tabbatar da cewa Bauchi ba ta faɗa irin wannan can hali ne na rikice-rikice ba. Rigakafi ya fi magani,” gwamnan ya yi gargaɗi.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa ya rawaito cewa zaman ya mai da hankali ne kan sa ido a kan dazuka da motsin mutane da kare wurare da al’umma ke harkokinsu da buƙatar samun rahoto daga tushe a faɗin jihar.
Waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da sarakuna da shugabannin jami’an tsaro da jami’an gwamnatin Jihar Bauchi.
