Tsohon shugaban NNPC, Mele Kyari ya shaƙi iskar ƴanci bayan tutsiye a EFCC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni sun tabbatar da cewa Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta sako tsohon Shugaban Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, bayan shafe tsawon lokaci ana masa tambayoyi a babban ofishin hukumar da ke Abuja.

Wata Majiya ta bayyana cewa Kyari ya amsa tambayoyi ne akan wasu batutuwa da suka shafi binciken ayyukan matatun man fetur na sassan Nijeriya, waɗanda aak ware wasu maƙudan kuɗaɗe daga kamfanin domin aiwatar da su.

An sako shi ne bayan kammala yi masa tambayoyi, amma kuma ana ganin zai ci gaba da bayyana a gaban hukumar domin bada ƙarin bayani akan zargin badaƙalar da aka samu a kamfanin a lokacin da ya ke shugaba.

A jiya Laraba Mele Kyari ya kai kansa ofishin EFCC domin gudanar da bincike akansa, bayan ta aika masa da saƙon gayyata.

Majiyoyi daga hukumar sun tabbatar da cewa zuwan Kyari ofishin bai rasa nasaba da bincike akan Dala biliyan 7.2 da aka ware na gyare-gyare matatun gwamnati, wanda a tsawon lokaci aka sanya a sahun kuɗaɗen da ake zargin sauya akalarsu daga kamfanin.

A kwana nan ne EFCC ta sanya Kyari a sahun waɗanda ta ke sanya ido akan zirga-zirgarsu.

Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan da Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta umarci a rufe asusun bankuna guda huɗu da aka alaƙanta su da shi bisa binciken badaƙalar kuɗaɗe.

By Babaji