Tura matan shugabannin ƙananan hukumomin Adamawa horo Turkiyya ya janyo cece-kuce

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tura matan shugabannin ƙananan hukumomi 21 na Jihar Adamawa birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya, domin halartar taron horarwa na mako guda kan jagoranci da cigaban al’umma ya janyo cece-ku-ce, inda ma’aikata, ’yan fansho, da ƙungiyoyin farar hula suka bayyana matakin a matsayin rashin hankali, almubazzaranci, da kuma cin zarafin al’umma.

An rawaito cewa, wannan tafiya mai cike da cece-ku-ce da rahotanni suka ce ta haɗa da wasu manyan jami’an ma’aikatar ƙananan hukumomi, ta haifar da fushi a jihar da tuni ke fama da matsalar bashin fansho, da rashin biyansu haƙƙoƙinsu, da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki, inda wasu ke ganin an kashe kuɗin jama’a ba tare da buƙata ba, yayin da wasu ke tambayar ko labarin gaskiya ne ko kuma sharri ne kawai.

Yayin da yake kare matakin, Suleiman Toungo, Shugaban ƙaramar Hukumar Toungo kuma shugaban ƙungiyar Shugabannin ƙananan Hukumomi ta Nijeriya (ALGON) reshen Adamawa, ya tabbatar da tafiyar.

Ya ce, “Mun yi irin wannan horo a watanni biyu da suka gabata, don haka ba na ganin wani abu da ba daidai ba a cikin tafiyar matanmu zuwa wajen horo. Su matanmu ne kuma muna buƙatar shawararsu. Muna kallon muhimmancin horar da su kan jagoranci, ba kudin da za a kashe a tafiyar ba.

“Su matanmu ne kuma muna buƙatar shawararsu, muna duban muhimmancin horar da su kan shugabanci, ba tsadar tafiyar ba,” inji Toungo, yana mai cewa shugabannin da kansu sun halarci irin wannan shirin watanni biyu kacal da suka wuce.

Duk da haka, da alama ra’ayinsa bai zo daidai da dukkan shugabannin ƙananan hukumomin ba. Wani shugaban ƙaramar hukumar Adamawa ta arewa da ya yi magana a ɓoye ya ce aikin ya rufe masa ido.

“Ina cikin barci sai na samu waya daga wani jami’in ALGON yana neman bayanin matata ta takardar biza, wannan shi ne karo na farko da na ji labarin aikin, babu wanda ya tuntuɓe ni, wannan kawai cin zarafin jama’a ne,” kamar yadda ya shaida wa jaridar.

Wannan fallasa ya haifar da tambayoyi masu zurfi game da yadda aka yi tafiyar, wanda ya amince da ita, da kuma ko an bi tsarin da ya dace.

Waɗanda suka fi yin kakkausar suka su ne waɗanda suka yi ritaya da kuma ƙungiyoyin kwadago, waɗanda suka ce shawarar cin fuska ce ga wahalar da suke sha.

Abubakar Shehu, ɗan shekara 75 mai karɓar fansho daga Yola ta Arewa, ya yi Allah-wadai da wannan shawara a matsayin “cin fuska ga dimokuraɗiyya.

“Mene ne matsayin shugabancin matan shugabannin ƙananan hukumomi? Hatta matar gwamnan ba a tura ƙasar waje don samun hora ba, wannan ba komai ba ne illa cin hanci da rashawa,” inji shi, inda ya buƙaci hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa ta EFCC ta shiga tsakani.

Wani mai ritayar da ya ƙi a bayyana sunansa ya yi kira ga Gwamna Ahmadu Fintiri da ya shiga tsakani ya miƙa lamarin ga hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa.

“Idan har gwamnatin jihar na son kiyaye martabarta, dole ne a binciki wannan badaƙala,” inji shi.

Lamarin dai ya zo ne watanni kaɗan bayan da gwamnatin jihar ta sanar da bayar da tallafin kuɗi naira biliyan 8 domin biyan basussukan fansho, amma duk da haka da dama daga cikin waɗanda suka yi ritaya sun ce ba su samu sauƙi ba. A gare su, tafiya ta Istanbul tana wakiltar abubuwan da ba su dace ba da kuma nuna halin ko-in-kula ga wahala daga tushe.

ƙungiyoyin ƙwadago sun ce lamarin na nuni da illolin cin gashin kan ƙananan hukumomin da ba a kula da su ba, inda suka yi gargaɗin cewa idan ba a sanya ido sosai ba, za a ci gaba da karkatar da kuɗazen raya kasa zuwa wasu matsaloli.

“Wasu daga cikin waɗannan matan ba su ma kammala makarantar firamare ba, amma duk da haka ana kai su Istanbul da sunan horan jagoranci,” inji wani ma’aikacin ƙaramar hukumar mai ritaya.

Nan da nan dai taƙaddamar ta rikiɗe zuwa badaƙalar mulki, inda ƙungiyoyin kwadago suka matsa lamba kan hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa da su binciki kuɗaɗen da ake kashewa.

“Mun aika da koke ga EFCC kuma muna da tabbacin hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa za ta sa baki nan ba da daɗewa ba. Wannan almubazzaranci ne da dukiyar al’umma a mafi girman ma’auni, kamar yadda wani babban jami’in kwadago a jihar ya shaida wa jaridar News Point Nigeria.

By ukarofi